Kishi Kumallan Mata 🤣

🤣 #Kishi_Kumallan_Mata 🤣
Matarsa ta ce “Kwana biyu na rabu da ganin abokin ka Abdul a gidan nan, Allah ya sa dai lafiya”
Sai ya ce “Mun ɗan samu saɓani da shi kwana biyu, amma zamu shirya.”
Sai ta ce “Allah Sarki…! Abdul mutumin kirki nasan yanzu haka laifin ka ne, ƙila kai ne ka ɓata mishi rai.”
Sai ya ce “ A’a ko kaɗan!, ce mishi nayi ina so in sayi mota da ƙuɗin da na samu a siyasar bana, shi kuma yake bani shawarar wai aure yakamata in ƙara tunda na samu dama,
Na nuna ƙin amincewa ta da shawarar shi, shi kuma yaji haushi ya ce kwata-kwata bana son ɗaukar shawarar shi, tun daga nan ko na kira a waya baya ɗauka.”
Sai ta ce “ Ƙyale ɗan banza!, Nifa dama kaf a cikin abokan ka sam ban yarda da wannan mai ruwan munafukan ba.”….🤣🤣
Copied