ko ya halatta mutam ya mallaki bindiga Don kare kan sa Daga mahara

Ko ya Halasta mutum ya mallaki Bindiga don kare kanshi Bindiga na daga cikin makamai masu matuƙar muni da haɗari a Nigeria dama duniya baki ɗaya.
Saboda zata iya yin ɓarna mai yawan gaske a cikin ƙanƙanin lokaci don haka Gwamnatin Nigeria tayi dokar data haramta ma mutane mallakar bindiga to saidai a wasu lokutan da dama mutane sukan buƙaci bindigar ko dan su kare kansu lafiyar su da dukiyar su lura da yadda ake ta fama da matsalolin tsaron da suka haɗar da satar mutane kisan gilla da sauran ayyukan ta’addanci.
To idan kana buƙatar bindigar ya za kayi
Na farko dai idan har kana bukatar bindigar dole sai an baka lasisi kuma a duk fadin Nigeria mutane uku ne kacal suke da damar bada wannan lasisin kamar yadda doka ta bayyana gasu kamar haka
Shugaban Ƙasa
Inspector General of Police
Kwamishinan ƴan Sanda na Jiha bayan ya samu izinin yin hakan daga gwamna.
Saboda haka idan kana buƙata abinda za kayi da farko Shine kaje babban ofishin ƴan sanda na jiha ko na ƙasa ka tambayi Department ɗin da suke bada wannan lasisin daganan zasu baka wani Form ka cika sannan ka biya kudin da ake biya na samun lasisin idan ka cika dukkan sharuɗan da ake bukata sai ka mayar da Form din bayan ka cika kenan daganan za’a baka lasisin siyen bindigar.
Sannan lasisin da aka baka dole zaka riƙa sabunta shi a duk Shekara A wurin sabunta shi dole zaka tafi da bindigar da kuma harsasan da aka yarda ka siya domin a duba shin kayi amfani dasu idan har kayi to dole sai ka bada bayanin yadda kayi amfani dasu ma’ana sai bayar da dalilin da yasa kayi harbi da bindigar Don haka idan an baka lasisin ba wai zuwa za kayi ka yita yin harbi anyhow ba