FadakarwaIslamic Chemist

KOH ME KWALLIYAR SARƘAR ƘAFA KE NUNI DASHI [ANKLET BRACELET]

KOH ME KWALLIYAR SARƘAR ƘAFA KE NUNI DASHI [ANKLET BRACELET]
┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Allah ya halicci yan adam kabila-kabila tare da mabambantan al’adu daga wasu kasashe zuwa wasu kasashen, jiha zuwa jiha, sannan gari zuwa gari, kai acikin gari daya ma aka iya samun mabambantan al’adu.

Adon sarka ko dan kunne abu ne mai tarihi a musulunci daga Mata ga Annabin Allah wato Annabi Ibrahim (AS) yayin da matarsa Sarat (Mahaifiya ga annabi Ishaq) ta sanyawa Matarsa Hajara (Mahaifiya ga annabi Isma’il) adalilin kishi domin bambanta kanta da ita tunda afarkon zamani Hajara ta kasance kuyanga ga Sarat kafin daga bisani taba annabi ibrahim shawarar aurenta. Tun daga nan mata suka sami wannan sunnah, saide a yanzu kwalliyar ta yawaita iri-iri har wasu sun ke banta da al’adu.

Sanya sarka kafa ka iya zama symbol na wasu abubuwan daban da saninka awani yankin na duniya irinsu india da sauransu.

Amma mu bisa al’adarmu ta yankin Africa (African culture) sarkar kafa alamace ta; KYAWU da kuma ARZIKI.

Saide kuma ayankin misra wato engypts kowanne rukuni na mata sun kasance suna sanyawa walau masu kudi ko talakawa amma sai ya zamto abunda ke bambancesu shine ta masu kudi ana yinta mafi kyawu sosai da kuma tsada.

Sannan inka gangaro bangaren mu na yammacin Africa, anyi zamanin da Mazaje kan mikawa mata su a matsayin alama ta soyayya ta shiga tsakani kamar yadda ada saurayi kanwa budurwa kyautar zobe.

Haka ma saurayi kan baiwa macen da yake gab da shirin aure bayan sa rana…

Haka a zamanin da mata kan kara da kararrawa ajikin sarkar dake ankarar da Maza cewa ga Mace nan ta shigo zata wuce, don haka su shiga taitayinsu ko kuwa ma su tashi su bata hanya inta shige sa dawo suci gaba da zama saboda girmamawa.

Haka de a Africa din wasu al’adun kuma ke amfani da sarkar kafa amatsayin alamu na Girmamawa da nuna jarumtar wannan Macen.

Wasu al’adun kuma na kallon sanyawa mace sarka akafa matsayin abune dake da mahimmanci ga lafiyarta.

Bansan taya yanzu mutane suka juya wannan dabi’ar ta sanya sarka ba a matsayin alama ta fasikanci ko karuwanci domin kaf tarihin Africa babu wannan.

Domin ko kasar Ghana ada babu mema sa sarkar kafa sai uwa ga basarakiya ko sarauniya ita kadaice ke iya ado dasu.

Haka masu rawa ta al’adu ko irinta koroso kan sanya sarkar kafa.

Amma akarshe de baki daya duk al’adun Afrika sun tafi kan sarkar kafa matsayin alama dake nuna mace tana da Aure.

Akwai tarihi mai karfi da kyawu agame da wannan al’ada ta sanya karfa akafa, inde har kana da matsala dame sanya sarka akafa toh kana da matsala da dukkan namiji mai sanya belt a mara tare da daura agogo, ko sarka hannu da wuya.

A matsayina namai kishin nahiyata ta Africa ina alfahari da al’adun mu, sarkar alama ce ta aure da kyawu ga sarakan matayen mu, basa samana ita don munin aiki.

Har yau har gobe jihohi irinsu sokoto, kebbi matayensu na irin wannan kwalliya haka jamhuriyar Nijar musamman matansu fulanin don haka karkaga matansu da ita ko kuwa sunzo ziyara jihohinku kuda bakwa irin wannan adon kuce zaku yanke musu hukunci kan yan madigo ko wasu fasikai ne, hakan kuskurene, ba abunda ya hada sarkar kafa da fasikanci, bakuma duk me sasu bace fasika.

Ku kiyayi yankewa al’umma hukunci, mu kiyayi abunda babu ruwan mu.

Wallahi in matarka nada sha’awa ko kai kana da sha’awa sayo mata ta saka ma, wanda yajefeta da wata kalma toh Allah yai hukunci a tsakaninsu.

Ku dena yankewa mutane hukunci da ance kace, ku dena 6atawa matan mu suna, wani kila tunda yake bai ta6a tunanin cewa bari yai binkice kan abu kaza ba… amma ya kware wajen yada karya cikin duhu game da abu.

In ma de hakan ne cewa kwai wasu nau’in Mata dake sata bisa manufarsu ta yaɗa ɓarna to lallai de abinda nakeso kasa ko kisa aranki lallai akwai waɗanda basu da wannan mummunar dabi’ar kuma suna sawa ne domin ado, kuma duk surutun nan baisa sun dena sawa ba saide ayi abari, amma har ga Allah ba fasikai bane, don haka kar aikin wasu yasa kaima dukkan Mata hukunci.

Kamar yadda nace musamman jihohin sokoto, kebbi, kasar Nijar da jihohi masu makwa6taka da Nijar din lallai ka sani har yau suna ado dasu sosai. Karkaje irin wannan gurare ka yankewa matayensu hukunci. Inkai haka bakai adalci ba, bakai aiki da hankali da ilimi ba.

Source:

https://www.google.fr/amp/s/ebonyx.co.uk/the-origin-of-african-anklets/amp/

https://www.google.fr/amp/s/www.modernghana.com/amp/news/867458/ankle-bracelets-the-art-of-african-culture-not.html

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button