LABARAI/NEWS

Kotu Ta Ɗaure Malamin Da Ke Wa’azi Tare Da Mata Shekaru Dubu 9 A Gidan Yari.

Kotu Ta Ɗaure Malamin Da Ke Wa’azi Tare Da Mata Shekaru Dubu 9 A Gidan Yari.

Kotun birnin Santanbul na Turkiya ta yanke wa wani malami mai wa’azi a kafar talabijin hukunccin ɗaurin shekaru dubu 8 da shekaru 658 a gidan yari bayan ta kamashi da aikata laifuka masu yawan gaske.

Malamin mai suna Adnan Oktar wanda ke da wani irin ra’ayi, na yadda wata fahimtar addini da ke ɗiga ayar tambaya game da asalin halittun duniya. Malamin ya kan tara ƴan mata masu nuna tsaraici su kewaye shi a lokacin da yake yin wa’azinsa.

 

 

a bara ne hukumomin Turkiya suka ɗaure shi shekaru dubu 1 da kwanaki 75 a gidan yari sakamakon kamashi da laifin cin zarafin mata da lalata ƙananan yara da damfara da kuma yunƙurin yi wa sojojin ƙasar leken asiri.

Sai dai babbar kotun ƙasar ta janye wannan hukuncin na bara, amma a yanzu, wata kotun birnin Santanbul ta yanke masa ɗaurin shekaru dubu 8 da shekaru 658 a gidan yari bayan ta tuhume shi da aikata laifuka da dama da suka haɗa da cin zarafin mata tare da take musu hakkokinsu kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar na Anadolu ya rawaito.

Malaman Musulunci na Turkiya sun sha caccakar malamin da suke yi masa kallon dan kungiyar asiri

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button