LABARAI/NEWS
Kotu Ta Hana Abduljalil Ɓalewa Bayyana Kansa A Matsayin Dan Marigayi Firaminista

Kotu Ta Hana Abduljalil Ɓalewa Bayyana Kansa A Matsayin Dan Marigayi Firaminista
Kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta hana Dr Abduljalil cigaba da kiran kansa dan marigayi Tafawa Balewa
Hakan na zuwa ne bayan da yayan marigayi Balewa, Mukhtar, Saddik da Umar suka yi kararsa a kotu
Alkalin ya ce wadanda suka gabatar da karar sun nuna hujjar cewa Abduljalil ba dan uwansu bane, shi kuma ya gaza nuna hujjar zamansa dan Balewa
Babban kotun tarayya na Abuja ta hana Abduljalil Balewa daga cigaba da kiran kasan dan marigayi firaiministan Najeriya na farko, Abubakar Tafawa Balewa
Kotun ta bada umurnin hana wanda aka yi karar ya dena kiran kansa ko wakilansa ko bayinsa kiransa da ko jika ko dangin Sir Balewa