ylliX - Online Advertising Network Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin wata 6 a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin wata 6 a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona

Kotu ta yanke wa budurwa hukuncin wata 6 a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona

Kotun Majistre 54 da ke unguwar Noman’s Land a jihar Kano ta yanke wa wata matshiya, Zainab Salisu Sheka hukuncin watanni shida a gidan yari bisa laifin yin sojan-gona.

Tun da fari, ƴan sanda ne su ka gurfanar da Zainab a gaban kotun, ƙarƙashin Mai Shari’a Ibrahim Mansur, bisa amfani da kayan ƴan sanda ta na bada hannu a danjar kan titin New Road da ke Sabongari.

Lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Barista Aminu Kawu ya roki kotu da ta karanto wa wacce ake tuhuma laifukan ta. Sai jami’in kotu Muhammad Zakirai ya karanto mata kuma ta amsa laifinta.

Sai dai kuma ta shaida wa kotun cewa aikin ne ya ke bata sha’awa shi ya sa ta yi Da ya ke yanke hukuncin, alkali Mansur ya yanke mata watanni shida a gidan yari ko tarar Naira dubu 50.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button