ylliX - Online Advertising Network KOWA YAYI DA KYAU ZAI GA DA KYAU, IDAN KA SHUKA ALKAIRI ZAKA GIRBI ALKAIRI. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

KOWA YAYI DA KYAU ZAI GA DA KYAU, IDAN KA SHUKA ALKAIRI ZAKA GIRBI ALKAIRI.

KOWA YAYI DA KYAU ZAI GA DA KYAU, IDAN KA SHUKA ALKAIRI ZAKA GIRBI ALKAIRI.

Ɗan Sandan Da Yaƙi Karɓar Cin Hanci Ya Samu Ƙarin Girma Da Kyautar Naira Milyan Guda…

Hukumar kula da ayyukan ƴansanda ta ɗaga likkafar Haziƙin ɗansandan nan wato DPOn Nassarawa jihar Kano CSP Daniel Amah daga Muƙamin CSP zuwa mataimakin ƙwamishinan ƴansanda (ACP) tare da bashi kyautar kuɗi Naira Milyan Ɗaya.

 

 

ACP Daniel ya samu wannan ƙarin girma ne bisa ƙoƙarin da ya nuna na tona asirin wasu batagari na abokan aiki waɗanda suka yi yunƙurin bashi cin hanci na miliyoyin kuɗi amma yace yaji tsoron Allah ya kuma yadda arziki da talauci da mutuwa da rayuwa duk a hannun Allah suke domin hakane yace ba zai karɓi wannan kuɗi ba, adalci kawai yake buƙata yayi.

Dalilin haka ne ma ƙwanakin baya shugaban kasa Muhammad Buhari ya karrama shi da lambar girmamawa ta Public Service Award, kazalika shima Shugaban Ƴansandan na ƙasa ya bashi Lambar Girma haɗi kuma da wadda Hukumar kula da aikin Ƴansanda ta bashi.

Ƙasa da wata biyu kenan da samun ƙarin girmansa na CSP sai gashi hukumar kula da ayyukan ƴansanda tayi masa ƙarin girma na musamman daga mukamin CSP da ya samu bada dadewa ba zuwa mataimakin ƙwamishinan ƴansanda (ACP)

Muna taya shi murna na sanya tsoron Allah a aikinsa fiye da komai
Allah ya taya shi riƙo yasa sauran Ƴansanda suyi koyi da abinda ya aikata na gudun duniya da ƙin goyan bayan zalinci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button