ylliX - Online Advertising Network ku bani shawara don Ni amarya ce - AMINCI HAUSA TV
Latest Hausa NovelsLABARAI/NEWS

ku bani shawara don Ni amarya ce

Ku Bani Shawara Don Allah Ni amarya ce

Ni Amarya ce na auri mijina yana da mata guda 1 da yara 6 Amma kowa gidanta daban Matsalar itace wallahi bana so naga yaje gidan uwar gida Saboda wallahi kishi yayi min yawa na kasa saita kaina kuma wallahi tana da hankali ta dauke ni da muhimmanci

kamar kanwarta amma bana kaunar naga mijinmu yaje wurinta ko Yadda yake yabonta so along the way ranar girkinta na dauki waya na kira ta Matar nan haka zata takura mishi yazo ya Kula dani

To amma Ni ban san me ke faruwa ba wata rana yace min idan ciwona ya tashi Kada in Kara gayamata aiba ita ke aure naba shi ne miji na shi zan kira

So idan nayi mashi karya ba na kirashi sai yaje chemist ya sayo magani
ya kawo min ya fita yaje gidan ta shine yanzu nayi
pretending twice inada aljanu sai inyi bige bige da fashe fashe in saka neighbors su kirashi Shi kuma

sai sukazo da matarshi suka daukeni naje na kwana a gidanta yanzu matsalan shine jiya danayi da yamma kawai sai yazo ya daukeni ya kaini wajen wani mugun malami wIh mutumin nan ya zaneni da dorina yace wai bakaken aljanu yake duka yanzu
yace a maidani ranar Friday zai min rukiya, wih ni Gaskiya tsoro nakeji kada yaje ya hallakani banida wasu aljanu wallahi yanzu don Allah yaya zanyi ku bani shawara

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button