LABARAI/NEWS

KUSKUREN DA AREWACIN NIGERIA ZA SU YI SHI NE SAKE BAIWA APC DAMA A 2023.

KUSKUREN DA AREWACIN NIGERIA ZA SU YI SHI NE SAKE BAIWA APC DAMA A 2023.

(1)–Babu Sababin Matatun Mai Guda Bakwai da Akayi Alkawarin Za’a Gina a NNPC…..
(2)–Babu Ma’aikatar ƙarfe ta Ajakuta…….
(3)–Babu Wutar lantarki ta manbila………..
(4)–Babu tashar Jirgin ruwa ta Baru……….
(5)–Babu Gyaran tsofaffin matatun Man NNPC
(6)–Babu jiragen Sama Na Nigeria Airways…..
(7)–Babu Matatun Mai Na Yankin Arewa………
(8)–Babu cigaba a harkar ilimi Ana Sace ɗalibai.. Ana Yajin Aiki..
(9)–Babu Sauƙi ta Ɓangaren Kayan Masarufi..komi ka taxa Yayi tsada Abinda talakawa ma za suci Yana gagarar su…….
(10)– Harkar Noma da kiwo ta lalace Saboda Mats’alar tsaro……
(11)–Babu canji a ta Ɓangaren Lafiya Asibiti Sunanan Yanda Suke Babu Wani chanji Saima ƙara lalacewa da Suka yi. idan talaka Baida ƙuɗin Sayen Magani Saidai Ya mutu……….
(12)–Babu tsaro An Gama lalata Arewa An ɗaurewa Ƴan ta’adda Gini kisa Suke Suna ƙona ƙauyuka da dukiyoyin jama’a. Suna Yiwa matan Aure da Ƴan Mata fyaɗe. Su sace jama’a idan An bada ƙunɗin fansa in sunga Dama Su saki Mutum in kuma Sukaga Dama Su kashe mutum Su keda iko Abin da Sukaga Dama Sukeyi Anrasa Mai taka Masu birki.. ….

Sun Riga Sun Gama Cutar da Arewa Shi Yasa Matasa Yara da Manya Suka Zama Ƴan cirani Ƴan Arewa Suketa kwarara kudancin Nigeria Saboda Su tsira da Rayuwarsu da kuma Neman Abinda Zasu ci kuma chanma kudun Walaƙantasu Ake Kamar Ba Ƴan ƙasaba… Anriga An Yiwa kasuwanci a Arewa giɓi Noma da kiwo Da ilimi Sun lalace makarantu da Yawa Arfe Suke Saboda Sace ɗalibai da Ake………

Babangida Musa Kano Dala,

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button