LABARAI/NEWS

Kwamandan Yan Bindiga Zai Auri Fasinjar Jirgin Kasan Abuja-Kaduna

Kwamandan Yan Bindiga Zai Auri Fasinjar Jirgin Kasan Abuja-Kaduna
Kwamandan ’yan ta’adda da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna na shirin auren wata budurwa daga cikin fasinjojin

Dan jarida Tukur Mamu wanda ke shiga tsakani ya kuma taimaka aka sako wasu daga cikin fasinjojin, shi ne ya koka kan shirin kwamandan ’yan ta’addan na auren Azurfa Lois John mai shekara 21

Tukur Mamu ya ce wata majiya mai tushe ta shaida masa cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba ’yan ta’addan za su aurar da budurwar nan ba da dadewa ba

su gaggauta yin abin da ya dace don kubutar da budurwar domin kada a maimaita abin da ya faru da Leah Sharibu
Ina sanar da gwamnati da kungiar CAN cewa na samu sahihan bayanai cewa idan ba hanzarta an ceto Azurfa Lois John mai shekara 21 ba, ’yan ta’addan za su aure ta yadda suka yi da Leah Sharibu

Wani kwamandansu ’yan ta’addan yana son ta don haka ya kamata a kula da dauki matakin da ya dace cikin gaggawa
Duk da cewa na san wannan bayani zai kawo damuwa ga ’yan uwanta da ’yan Najeriya baki daya, yin hakan ya zama wajibi don gudun kada a maimaita irin na Leah Sharibu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button