ylliX - Online Advertising Network Kwankwasiyya Tiktoker's Group D. Sun Biya Kudin Makaranta Ga Ɗalibai 70 Har Na Tsawon Watanni Biyar - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Kwankwasiyya Tiktoker’s Group D. Sun Biya Kudin Makaranta Ga Ɗalibai 70 Har Na Tsawon Watanni Biyar

Kwankwasiyya Tiktoker’s Group D. Sun Biya Kudin Makaranta Ga Ɗalibai 70 Har Na Tsawon Watanni Biyar

Shararriyar ƙungiyar nan dake tallata manufofin Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso a kafar Sada Zumunta na TikTok Kwankwasiyya Tiktoker’s, karkashin jagorancin Kwankwasiyya Tiktoker’s Team D. Sun Biya kuɗin makarantar ɗaliban islamiyyu 70 na tsawon watanni biyar tare da basu tabarmin karatu.

Wannan Team na Kwankwasiyya Tiktoker’s Team D. Sunyi wannan namijin kokarin ne ga ɗaliban makarantar Kawon Lambu, duk a cikin kokarin ta na koyi da jagoran Kwankwasiyya kuma Shugaban ƙasar gobe da iznin Allah Engr Dr Rabi’u Musa Kwankwaso.

An gudanar da wannan abin Alkhairi ne karkashin jagorancin Haleema Idris jagoran Kwankwasiyya Tiktoker’s Team D. Da dukkan mataimakan ta, bisa kyakkyawan shugabancin shugaban ƙungiyar na ƙasa gaba ɗaya Aminu Abdullahi (Alhaji Warkal) da Jagoran Tafiyar Ambassador Nura Nitel, da mataimakan su.

Kamar yadda kuka sani halin jagoran mu ne tallafawa marasa ƙarfi da marayu da Talakawa hakan yasa wannan kungiya ke koyi dashi wajan aiwatar da ayyukan Alkhari ga al’umma.

Kwankwasiyya Tiktoker’s Yan Amanar Kwankwaso suna buƙatar addu’o’in ku domin suci gaba da ayyukan Alkhari ga al’umma da kawo cigaba a tsakankanin al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button