LABARAI/NEWS

Kwankwaso ya mayarda mutane mahaukata suna yawo da jarhula kamar Tsuntsaye – kalaman Aminu ringim a baya.

Kwankwaso ya mayarda mutane mahaukata suna yawo da jarhula kamar Tsuntsaye – kalaman Aminu ringim a baya.

Daga Umar Dajani

Wato da ace ban samu tarbiyar kare mutuncin kaina ba tun daga gidanmu, da ace Allah bai hadani da jagora kuma shugaba mai daraja da akida da tsoron Allah irin Sule Lamido ba da watakila yanzu nima ku ganni da irin wannan abar a kaina.

Wallahi Allah banyi rubutun nan dan cin mutunci ko wulakanci ga Aminu ba, sai don tarihi yana da kyau saboda yan’ baya suji don suma su guji yin abin kunya a siyasa.

A lokacin da muke cikin gwamnati ina yawan saka jar hula a kaina, amma duk lokacin dana sska jar hula na shiga office din Gwamna muddin Aminu yana ciki sai ya tsokaneni yace, Sir ga Umar fa da jar hula sai Lamido yayi shiru.

Rannan abin da yayi yawa sai Sule Lamido yace Aminu wannan hular ai irin ta Babansa ce, tun daga ranar Aminu ya dena damuna akan saka jar hula.

Akwai wata rana da muka raka gwamna Sule Lamido gidan gwamnatin Jihar Kano don dansa daya aurar, a tsakar gidan gwamnatin sai mukaga mutane da yawa da jajayen huluna sai Aminu yace Umar don Allah dubi hauka.
Mun hau sama mun shiga ofis din Gwamnan Kano Kwankwaso sai mukayi arba da Gwamna Badaru a cikin ofis din a zaune kafin Allah ya zama gwamna, abinda Aminu ya fara cemin shine Umar kaga munafurci ko? yace wallahi Umar bana son Kwankwaso ko kadan saboda bai iya siyasa ba sai shirme.

Har yanzu ina tuna lokacin da Gwamna Sule Lamido yayi lacca a Kano har ya soki yadda ake siyasar jar hula, muna dawowa Dutse Aminu ne mutum na farko da yace Sir wallahi ka birgeni kawai Kawankwaso ya maida mutane mahaukata kullum suna yawo da jar hula sai kace tsintsaye.

Ikon Allah sarki goma zamani goma, Jama’a yau ga Aminu da jar hula, shin menene matsayar sukar Kwankwaso da jar hula da yayi a baya?

Allah karka jarabceni da yin biyayya ko marawa makaryacin shugaba baya ko wanene a Duniya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button