LABARAI/NEWS

LABARAI

Rashin Ruwan Famfo: Ganduje zai fara rabon ruwa a unguwannin Kano

LABARAI

Rashin Ruwan Famfo: Ganduje zai fara rabon ruwa a unguwannin Kano

Gwamna Ganduje zai fara raba ruwa a unguwannin Kano saboda ƙarancinsa da ake fuskanta.

Ganduje ya bayyana hakan ne a yau Lahadi yayin da ya ziyarci matatar ruwa ta Challawa.

Yayin ziyarar Ganduje ya buƙaci al’ummar Kano da su ƙara haƙuri a kan matsalar ruwan shan da ake fama da ita, inda ya ce nan bada jimawa ba zata zama tarihi.

Ganduje ya ce daga gobe Litinin motocin tankunan ruwa za su fara zagaye domin rabawa jama’ar gari.

Dangane da matsalar ƙarancin ruwan kuwa, Gwamnan ya ce, an kafa kwamitin da zai yi nazari kan yadda za a lalubo bakin zaren.

Sannan za a gyara injinan wutar lantarkin da ake aikin tunkuɗo ruwa dasu.

Wakilyar mu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa Gwamna Ganduje ya kuma ziyarci hukumar samar da ruwan sha a yankin karkara.

Wannan dai shi ne karon farko da Gwamna Ganduje ya ziyarci matatar ruwan, tsawon shekaru bakwai da ya zama Gwamna

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button