Fadakarwa

LABARI MAI CIKE DA DARASI DA SOSA ZUCCIYA

LABARI MAI CIKE DA DARASI DA SOSA ZUCCIYA..

Wani Miji ne ya maari Matarsa a fuska tafara kuka tana cewa Wallahi sai nakai ‘kararka.
YACE MATA: Waya faɗamiki zanbarki kifita?

TACE: Kana tsammanin inka tsare kofa ka kule windows kana ga zaka hanani kai qaranka ne?

YACE: Ta Ina zaki kai ‘karan?
TACE: Zanyi magana ne.

YACE: Wayoyinki duk suna guna. Kiyi duk abinda zakiyi.
Sai tanufi hanyar banɗaki sai shi kuma yaje ta bakin window din banɗaki don a tunaninsa zata fita tanan ta gudu ta kai ‘karansa, yajima yaga batayi niyyar haka ba. Kawai sai ya zagayo ta bakin ‘kofar sai yagaa tafito ta banɗakin jikinta na ɗiga da ruwa tana murmushi.
TACE: Zan kaika ‘karane gun wanda na rantse dashi wanda rufe ‘kofarka ko Window ko kuma hanani amfani da waya bazai hanashi jin kukana ba.

Sai jikinsa yayi sanyi yakoma gefe yayi shiru yana tunani.
Taje tayi kabbarar sallah, tajima acikin sujjada yana ta kallonta. Bayan ta Idar da Sallar saita ɗaga hannunta zata qara da addu’a, kawai sai ya taso ya riqe hannunta.

YACE MATA: Yanzu munanan Addu’an da kikamin a Sujjadan basu isaba saikin ‘Kara wasu?
TACE: Kana tunanin zan tsaya da Addu’a ne bayan abinda kamin?
YACE: Wallahi fushi ne yasani haka banyi niyyar haka ba.
TACE: Toh don hakan ne bazan daina maka Addu’ar ba! Addu’ar tawa akan shaidan ne, da ya zugaka kayimin haka.
Ni ba wawiya bace da zanyi munanan Addu’a ga Sanyin Idaniyata Kuma Farin cikin Zuciyata.
Sai Ya fashe da kuka, ya sumbanci(kissing) hannunta…
YACE: Na miki Alkawari bazan qara taɓaki da wani cutarwa ba daga yau.
Wannan Itace Mace Tagari wanda Allah da Annabi suka mana wasiyyar mu Aura.
Kizame masa baiwa zai zame miki bawa…..
Alllah ka Azurtamu da Mata Nagari….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button