LABARAI/NEWS

LABARI MAI DADI: Zulum ya yi wa ma’aikata karin 200% a albashi, ya raba kudi da kayan azumi saboda rage musu wahalhalun azumi.

LABARI MAI DADI: Zulum ya yi wa ma’aikata karin 200% a albashi, ya raba kudi da kayan azumi saboda rage musu wahalhalun azumi.

Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum ya bada sanarwar yi wa wasu ma’aikata karin albashi Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce ma’aikatan da ke karbar N10, 000 a wata za su samu karin 200%.

Bayan haka an rabawa wadannan Bayin Allah kayan abinci, kudi da kuma tufafin sallah a Maiduguri.

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bada sanarwar yin karin albashi ga kananan ma’aikatan da su ke kan aikin wata-wata.

Jaridar Daily Trust ta ce Mai girma gwamnan ya bayyana wannan ne a ranar Litinin. Duk wanda yake karbar N10, 000 a wata zai samu karin 200%.

Farfesa Babagana Umara Zulum ya bada wannan sanarwar ne a lokacin da ya sa ido wajen rabon kayan abinci da kudin da aka rabawa ma’aikatan.

Sanarwar ta ce wadanda suka amfana su ne ma’aikata 285 da ke goge gidan gwamnati, da wanda hukumar BOSEPA ta dauka aiki domin sharan gari.

Abubuwan da aka rabawa ma’aikata Kowane ma’aikaci ya samu buhun shinkafa, kilo 10 na sukari, lita biyar na man gyada, kilo biyu na nama, da turmin zani da yadin shadda da N20000.

Da yake jawabi a jiya, Babagana Zulum ya jinjinawa wadannan ma’aikata da suke kokari wajen kula da gidan gwamnati, don haka ya taimaka masu.

Gwamna Zulum ya na kallo aka raba kayan abincin da kudi ga wadannan kananan ma’aikatan.

Abin da aka kashe wajen wannan rabon ya kai N5.7m. “Dole in ce ina alfahari da gaba dayanku saboda irin namijin kokarin da ku ke yi wajen tsabtace da kula da gidan gwamnatin nan yadda ya kamata.”

“Ramadan aka shiga, kuma daga gida ya kamata a fara, shiyasa na zabi in taimaka maku da abinci da kudi domin hidimarku da ta iyali a watan nan.” – Babagana Umara Zulum

Gidan rediyon FRCN sun rahoto gwamnan na jihar Borno ya na kira ga ma’aikatan da su dage wajen yi wa jiharsu da fadin Najeriya addu’ar zaman lafiya.

Me Zakuce Akai

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button