LABARI ME DAƊI Yan sandan Legas Sun kama Motoci Maƙare Da Alburusai A Ikorodu Za Akai Jihar Katsina

LABARI ME DAƊI Yan sandan Legas Sun kama Motoci Maƙare Da Alburusai A Ikorodu Za Akai Jihar Katsina
Rundunar Yan sandan jihar Legas, ta Cafke Wasu Motocin Bas Guda biyu Makil Da manyan Katosai Masu Rai, Tarwatsa Babura Guda Uku A Estate Poromope, Kan Titin Ijede, Ikorodu, Jihar Legas.
A Wata sanarwa Da jami’in Hulda Da Jama’a Na Rundunar Ƴan Sandan jihar, Benjamin Hundeyin Ya Sanyawa HannuA Ranar Asabar, jami’an sashen Na Ikorodu Suka Kama Su
Hundeyin Ya ce, Bincike Na Farko Ya Nuna Cewa Waɗanda Ake Zargin, Tukur Abdullah Mai shekaru 35, Muazu Telim Mai Shekaru 50 Da Ɗahiru Idris Mai shekaru 36 Suna Kan hanyarsu Ta Zuwa jihar Katsina.
Waɗanda Ake zargin, Da kayayyakin Baje koli Da kuma Motocin, Masu LAmbar Rajista KMC 438 YK Da KMC 394 XF An Miƙa Su Hedikwatar Rundunar Ƴan Sandan jihar Legas, Ikeja Domin Ci Gaba Da Bincike.