LABARAI/NEWS

Labarin Tsibirin Bamuda Mai Matukar Ban Al’ajabi wato fadar shedan

Labarin Tsibirin Bamuda Mai Matukar Ban Al’ajabi wato fadar shedan

Tsibirin Bamuda
Duk da cewa duniya abubuwan mamaki basa Karewa a cikinsu ba tare da Dan Adam ya fahimci musabbabansu ba Tsibirin Bamuda (Bermuda Island ko Bermuda Triangle) ne kadai ya fi shahara a bakunan mutane sanadiyyar haka

Wannan shahara ta samo asali ne daga nahiyar Kudancin Amurka South America a hankali labarin ya ci gaba da yaduwa zuwa sauran kasashen duniya

 

Manyan ababen mamakin da ake ikirarin suna faruwa a muhallin tekun da wannan tsibiri yake sun hada da bacewar jiragen sama masu dauke da fasinjoji yan kasuwa ko na soji da jiragen ruwa – manya da kanana da na shawagi Idan suka bace a galibin lokuta ba a ganin buraguzan jirgin balle a kaddamar da bincike kan dalilan da suka haddasa faruwar hadarin

 

Wannan al’amari abin al’ajabi a cewar masu bayar da labarai bai tsaya a bacewar jirage tare da rashin ganin buraguzansu kadai ba har da wasu labarai masu caza kwakwalwa kan irin yanayin da tekun ke kasancewa na launi da kuma dulmuya a wasu lokutan

ko kuma wasu irin dabi’u da ake ikirarin gira-gizan da ke saman teku ke shiga a yayin aukuwar hadarurrukan da suka fara faruwa shekaru kusan 200 da suka gabata

 

Ire-iren wadannan labarai sun samo asali ne daga irin jawaban da masu lura da na’urar filin saukan jiragen sama da ke tsibirin ke bayarwa Ko wadanda ake tarawa wajen binciken da hukumomin gwamnatin Amurka da ke lura da ire-iren wadannan hadarurruka ke yi

Da wannan marubuta suka sa wa wannan muhalli suna The Bermuda Triangle’ (Kusurwar Bamuda) ko kuma The Debil’s Triangle (Kusurwar Shedan)

A halin yanzu da dama cikin wadanda suka taba jin labarin wannan bigire na Bamuda sun yarda cewa wani wuri ne mai cike da almara, kamar yadda galibin turawa masu bincike suka fada. Da kuma cewa babu wanda ya san abin da ke haddasa wannan al’amari, sai Allah (ga wadanda suka yarda da Allah kenan), ko kuma dabi’a ta shu’umcin wurin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button