Islamic Chemist

LARURAR BARGAJEWAR ƊABI’U, SHAUQI DA TUNANI, [SCHIZOPHRENIA]

LARURAR BARGAJEWAR ƊABI’U, SHAUQI DA TUNANI, [SCHIZOPHRENIA]
┈┉━┅━━💕💗💕━━┅━┉┈

Sikizofreniya cutar kwakwalwa ce dake canza ɗabi’u, nazari da tunanin ɗan adam, koma gushewar hankali ya rika abubuwa bambarakwai.

Alhalin cutar ta soma ahankali tun farko batare da mutum aka ran kansa ya fahimci cewa bashi lafiya ba, ko kuwa yana tunkarar ciwon ƙwaƙwalwa ko rangwamen Hankali ba. Tana bayyana har a yara ma basai manya ba.

Sannan cutar tana da tasiri da gado wato bin family tree, wato da wuya a dangi ka sami me cutar mutum ɗaya, kamar gado suke.

Saide wani lokacin takan faru ko ba gado dalilin tangarɗar halitta tun aciki kafin a haifi mutum, ko idan mahaifiya tai wani ciwo yayin goyon ciki, ko doguwar naquda, ko kuma irin muhallin da mutum ya taso ya gamu da wani ciwo tun yana ƙarami ko poison.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Wannan larurar na daga Manyan cuttukan ƙwaƙwalwa da kansa Mutum ya kasa yin:

 • Tunani sak
 • Kasa jin shauƙi,
 • Annashuwa,
 • Rashin son magana
 • Kasa ji ko nuna Farin ciki
 • Kasa shiga Mutane
 • Jin cikin kansu komi a hautsine
 • Ko ya rika dariya babu dalili
 • kasa ayyukan yau da kullum
 • Kasa jin cewa an damu dashi
 • Ko rashin jin kuzari a jika,

Kuma takan sanya Mutum kasa yin mu’amala da mutane. Kai in abu yai ƙamari mutum kanji kwakwalwarsa na bashi umarni aikata wasu ayyuka munana na rasa rai ko cutar da wasu.

A irin hakane mukanji ance Mutum yaje makaranta ko gurin taruwar mutane ya buɗe wuta ya kashe na kashewa, ya jikkata wasu a ƙarshe kuma ya harbe kansa da kansa. Ko ace mutum yasha guba ya mutum.

Galibi ba dare ɗaya sukan faru ba, kwai alamun taɓuwar kwakwalwa da mutum kan nuna tun farko amma inba kusa da masu ilimin sanin ɗabi’un ɗan adam yake ba baza aɗauka sansomin larura bane tun kafin ma yakai ga mugun aikin.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

WASU KEƁANTATTUN SUFFOFIN CUTAR

Daga waɗannan alamun kwai [Hallucinations da kuma Delusion].

Hallucinations: shine ne kamar sumbatu amma ba iya ta fatar baki ba, domin ido da kunne duk ana sumbatu dasu. Harma baki da hanci.

1]- BABAL HALUSINESHIN:

Wato ake jin mutum yana sumbatu maganganu shi kadai ko motsa baki kamar yana faɗin wasu kalmomi ta fatar bakin ya riƙa magana da kansa shi kadai yana dariya ko murmushi, ko kuwa aga ya ware guri guda yana magana bakinsa na motsi amma babu me iya jin me yake faɗi kullum cikin haka. Amma de ba duka ba zagi, ba komi, fes babu ƙazanta. Normal harkoki wasu duk ana yi da mutum

2]- BIJIWAL HALUSINESHIN:

Wannan wasu abubuwa mutum zai riƙa bayanin yana gani da idonsa wanda ku dake tare dashi bakwa gani, yana iya cewa ga kaza da kaza amma ku duk bakwa gani, ko yake suffanta muku wata sufa.

3]- ODITORI HALUSINESHIN:

Mutum zai rika jin maganganu ne da shi kadai yake ji, na umarni yai wani abu, ko kuwa koda babu qara agu sai ya rika ce muku bakwajin abu kaza? Ko kuwa ga wata magana da ake fadi, ko yace yaji ana bashi umarnin yaje gari kaza.

4]- NESAL : Mutum ya rika korafin yana shaqar wani ƙauri, wari ko ƙamshi na wani abu da Sam babu shi kusa ko nesa.


Sai kuma Ɓangaren “DELUSION”

DILUSHUN: Shine Ruɗun kwakwalwa ne da babu abu ko kuwa mutum baida abu amma zai riƙajin yana da abin, ko bai mallaki abu ya riqa jin kwai abin, ko danganta kansa da wasu mutane bayan sam babu haɗi a zahiri.

Daga cikin kashe-kashensa akwai:

 1. FARANOYID DILUSHUN:

Shine mutum ya riƙa jin kamar kwai wasu wane da wane dake can suke ɓatasa, ko shirya yadda zasu cutar dashi, ko kasheshi, ko kuwa Babarsa ko babansa na masa zagon ƙasa kan wani abu domin wargaza rayuwarsa.

Amma a zahiri shi bakowa ma bane sai banza domin baima da abinda wani ya damu dashi inka kallesa. Kaga soyayya ta uwa da ɗa amma inya zo gaban likita wani na iya cema shifa ya dena cin abincin babarsu ko Matarsa ne saboda yaji tana magana da abincin cewa inyaci shi ya shaqesa, ko yace babarsu kashe shi take son yi duk da bata bayyana masa.

Haka de tunani na shirme da a zahiri bazai taɓa yiwuwa ba ko babu haɗi. Ko kuwa kaga mutum ko a media kullum baida aiki sai zancen a rabasa da masu hassada amma fa babu me masa hasaadar a zahiri kurum kwakwalwarsa ke fadamasa cewa wani na masa hassada, ko kuwa wani najin haushin wata ɗaukakar sa, Amma fa a zahiri inka Sansa zakasan ko kwana yai ba’a gansa ba babu wanda ya damu da ina yake a gidansu ballantana zancen hassada ko cutar dashi!


 1. Ai DIYA OP REFARANS

Sukan ji cewa duk wani abubuwa da ake tattaunawa a gidajen Radio, jaridu, talbijin duk akansu ake tattaunawa, inma film ne akansa aka shirya film din, ji kurum yake komi don shi ne, ba bayanin komi bane sai nasa ko nata.

Haka wasu kuma kan danganta kansu musamman cikin Mata kaji Mace na bayanin shugaban kasa saurayinta ne, gwamna kaza, minista kaza, ko wasu manya-manya duk ta rika danganta cewa soyayya suke da ita.

Hakama namiji kan riƙajin yar gidan wane soyayya take dashi, ko kuwa in wata na kulasa ko kula abinda yake ya rika jin lallai cewa soyayya take dashi alhalin Sam babu haɗi.


 1. EKSTANAL LOKUS OP KWANTUROL:

Shi wannan a tsakanin shekarun karatu yafi bayyana, su irin wannan ɗaliban kurum sun gamsu in sunyi nasara ko faɗuwa a jaraba tohfa hakan ya faru ne saboda tasirin wani abu daban kamar suka: Sa’ar da wani boka ya bayar, ko zaluncin malami ne ba faduwa sukai ba kayar dasu akai, ko kuwa son kai ne, ko kuwa rashin kwarewar malamai, domin wani ka iya jin yama fi malamin sanin komi.

Ko kuwa inma ba ɗalibai bane cikin Maza ko Mata sun lamince ko ciwon kai sukai toh wani ne yai musu asiri.


 1. TOT INSA’SHIN:
  Irin waɗannan mutanen Kanji cewa abinda ke ransu ba nasu bane ra’ayi ne dake ran wasunsu kurum ake cuso musu domin su su faɗa. Ko abinda suke fada ko suke furta wa bafa sune ke maganar ba a’a maganar wani ce aka cusa ransu aka sasu suke faɗa.

 1. JELOS INSA’SHIN:

Shine kasa bijire wa zuciya umarnin da take ba mutum na nuna tsananin kishi: Wanda wannan kan tada zaune tsaye musamman tsakanin ma’aurata, rigingimu, zargi da ƙazaman laffuza.

Misali: sune zakaga duk inda Miji ko Mata ta shiga ɗaya Allah-Allah yake yasani, wane daga ina kake, wane naji wayarka tai qara waye, Waye kike magana dashi, Ko mutum ma ya rika zargi kuruquru cewa Matar ko Mijinta na cin amanar ta, bayan sam babu.

Ko kuwa hatta yan uwanta na jini kaga miji bai son su raɓi Matarsa ko su zo gidan ballantana kuma kawaye, Haka itama ko waye ya raɓi mijinta musamman Mace tohfa tana ganin damar ta kashe.

Anyi wani film din hausa “Namijin kishi” toh wannan dabi’ar da aka suffanta Namiji exactly na daga abinda nake kokarin haskawa ga irinsu mahaukacin kishi.


 1. GIRANDIYOS DILUSHIN:

Mutum ya riqa jin shi wani ne, sama yake da kowa kuma yafi karfin kowa ya wulakanta shi, wato de ya gagara, kuma inma yana da yar wadata yakan rika ganin hakan ne matsayin wani tarin arziki da ko me kudin duniya bai kaisa arziki ba kurum mutane ne basu lura ba, ko ya rika jin shi yafi kowa asali da cancantar abubuwa da yawa na rayuwa.

Ko kuma yake jin yafi kowa tarin ilimi da fahimtar gaskiya, kowa kan kuskure yake shi kadai ne kaf gari, I ko jihar ko ƙasar ke kan daidai tare da ilimin da babu kamar sa.

Ma’ana: a komi sukan wuce gona da iri daga ainishin yadda suken, koda suna da wata yar nasaba da abinda suke danganta kansu, sukan rika sakin zan tuka na katoɓara wani abin ma Allah ne kadai keda hurumi kansa. Toh ahankali alama ce ta suna tunkarar Schizophrenia.


 1. DILUSHUN OP JULT:

Su masu irin wannan zargin kai garesu kan wani abu da ya faru kamar lefinsu ne da basu yi abinda ya kamata ba. Kamar girgizar kasa, ko gobara awata ƙasa can, ko hatsarin ababen hawa yakan ji cewa laifin sa ne, duk da babu wani haɗi kila baima san inda abin ya faru ba. Kurum de zargi yake duk wani abu dake faruwa mara kyau a gari ko ƙasa laifin sa ne.


SOMATIK DILUSHUN

Su irin wannan kullum shine sun yarjewa kansu cewa lallai cikin kayan cikin su wani abu ya ruɓe ko ya lalace baya aiki yadda ya kamata, ko kuwa cibiyar su, ko bakinsu ba yadda yake ya kamata ya kasance ba, ma’ana da daidai yake dana sauran mutane ba. Hakama kunnuwa ko idanuwa, ko su rika zargin lallai suna da cutar cancer likita ne yaki yadda su sun lamince suna da ita, ko kuwa kwanyarsu ta ruɓe ko kwai wani abu dake rayuwa cikin jikinsu. Da sauransu.


TOT BURODIKASTIN

Su kuma wannan rukunin kan riƙajin cewa ansan meke cikin zuciyarsa, kamar duk abubuwan da yake sakawa ansani, Sam baya son zama cikin mutane ko kuma ware kansa za kaga yana yi koma yake qin zuwa makaranta. Da sauransu

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈

Wannan kadan daga wasu suffofi da masu cutar Schizophrenia ke fuskanta kenan, amma medical doctor (psychiatrician) ne kadai ke iya confirming na ciwon domin ba iya alamomin ake kallo ba. Kwai sauran abubuwa da lokacin da mutum ya shafe cikin matsalolin kafin a tabbatar, sannan ba sharadi bane duk sai mutum ya tattara wadannan alamomin.

┈┉┅━━┅┉┈┈┉┅━━┅┉┈
Sadly, cutar bata da magani da za’a warke din din-dun, saide ana haɗawa mutum magunguna ne domin magance alamomin da yake fuskanta domin saukaka masa rayuwa. Ya iya achieving abubuwan yau da gobe.


Don haka in kuna da yan uwa masu wasu daga cikin waɗannan ɗabi’u ai kokarin sadasu da neuropsychiatric a manyan asibitoci FMC, Teachings, Specialist hospital Ko Psychiatric hospitals domin samun tallafin likitoci.

✍🏼

[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button