Islamic ChemistLABARAI/NEWS

LARURAR GUBAR ABINCI (FOOD BORNE ILLNESS)

𝐋𝐀𝐑𝐔𝐑𝐀𝐑 𝐆𝐔𝐁𝐀𝐑 𝐀𝐁𝐈𝐍𝐂𝐈 [𝐅𝐎𝐎𝐃 𝐁𝐎𝐑𝐍𝐄 𝐈𝐋𝐋𝐍𝐄𝐒𝐒]

Gurɓataccen abinci na daga larurar dake kisan farat daya domin duk jinkirin sekons guda na agogo kara tsananta jigatar wanda yaci gubar ne. Wannan guba ka iya zuwa daga gurbataccen abinci, ruwan sha, madarar kanti, lemukan juice, ko wasu sinadarai na hade lemukan wadanda suka riga suka gauraya da kwayar cutar bakteriya, birus, farasayit ko kuma gubar kai tsaye wato toxins.

Wadannan kwayoyin cuta ko guba ba abune da idon zai iya ganinsu ba, haka kuma bai zama dole abaki kaji dandanonta ba. Galibi guba bata da dandano ko kala (is tasteless and colorless), shyasa barnar inta samu tarin mutane bakyau, lokaci guda daruruwa na iya kwanciya, domin komi wuya da ace da wari ko dandano to da inguda yasha zai iya sanar da saura.

Wannan tasa tsakanin da akasamu 6arkewar annobar a kano abun bai 6oyu ba saida kowa yasan anshiga masifa.

𝐌𝐄 𝐀𝐊𝐄 𝐍𝐔𝐅𝐈 𝐃𝐀 𝐆𝐔𝐁𝐀𝐑 𝐀𝐁𝐈𝐍𝐂𝐈

Idan akace Guba; ba ana nufin wani sinadari da aka barbadawa mutum cikin sani ba don yaci ya mutu ba kurum. A’ah abunda aka saba ci normal ma ka iya zama guba watarana; Kamar madarar data expire, ko abincin da ya kwana akaci batare da andumama ba ka iya zama guba musamman idan kwayoyin cuta sun hau kai, haka ma sinadaran hada lemuka in sun wuce wa’adinsu wato expiring data amma ha’inci yasa aka canza musu packet ko aka goge expiring din mutane suka rika sha shima na zama guba.

Haka idan kasai packet din lemo ajiki aka rubuta ahada dukkan packet da LITER 5 na ruwa amma kai kace in aka hada iya LITER 1, ko 2 Ko LITER 3 yafi dadi toh inkasha ka 6arke da gudawa ya zama guba amma da laifinka domin baka bin instruction. Don haka wadannan rubutun na jikin packet din abubuwa ba abanza ake yinsu ba… shiyasa koda da Nafdac number inka ki kiyayewa kana iya kwana aciki.

Haka ma magani da akesha yau da kullum ka iya zama guba idan aka shasa daka, ko akasha fiye da abunda likita ya tsara asha a tunanin cewa ai in ansha da yawa afi saurin samun sauki.

Ko kuma ruwan sha mara kyau da ya gurbata da kwayoyin cuta, ko kuma ruwan roba ko na leda da basu sami cikakkiyar kulawa ba ko kuka aka sa sinadarin chlorine na kashe kwayoyin cuta fiye da kima acikinsu nan ma ka iya zama guba.

𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐃𝐀𝐊𝐄 𝐍𝐔𝐍𝐀 𝐀𝐍𝐂𝐈 𝐀𝐁𝐔 𝐌𝐀𝐈 𝐆𝐔𝐁𝐀

Alamun farko dakan nuna anci abu me guba a awa ta farko sune; tashin zuciya, amai, da gudawa haka ɓakatattan za’a fara akai akai ba daga kafa. Kafin ka ankara karfinka ya tafi. Saide wani lokacin in gubar kadance in mutum ya fatattaka wannan kashin wani toh shikenan sai aji tsit idan gubar bame illa bace sosai.

Wata gubar kuma ba nan take ko ranar da kaci zata fara aiki ba wata sai ankwana koma anyi sati, toh amma duk alamun dayane, domin

Da anyi rashin sa’a anci da yawa ko kuwa garkuwar jikin mutum ta gaza yakar gubar tohfa saide abunda yai gaba, daga nan komi zai qaru:

■- Zazza6i me zafi fiye da tempreture 38°c

■- Yawan tashin xuciya

■- Gudawa sosai hade da jini ta fiye da kwana 3

■- Fitsarin da Jini

■- Aman jini, domin ruwa ruwan cikin duk ya qare yanzu hatta amana na wahala ne

■- Ciwo tare da murdawar ciki me zafi.

■- Alamun karancin ruwa; Yawan kishirwa, bushewar baki, karancin fitsari, kasala me tsanani, ganin jiri,

■- Canzawar kalar fata zuwa blueish alamun karancin iska cikin jini.

■- Alamomin abun ya fara shafar kwakwalwa: Gani hazo-hazo, jin hannayenka kamar ba ajikinka suke ba kamar ana tsikarinsu tare kasa mikewa ataka saide mutum akwashesa.

Ciwon yai kama da cutar kwalara saide shi wanda yaci gubar shi kadai ne ke fama, sa6anin kwalara da inkai wasa ko shaqa kayi yanzu ne zance zai canza

𝐌𝐄 𝐘𝐀𝐊𝐄 𝐉𝐀𝐖𝐎 𝐌𝐀𝐂𝐄-𝐌𝐀𝐂𝐄 𝐈𝐍 𝐀𝐍𝐒𝐀𝐌𝐔 𝐀𝐍𝐍𝐎𝐁𝐀 𝐇𝐀𝐊𝐀

Babban abunda ke kashe mutane shine karancin ruwa ajika (Dehydration), domin kana ta kwara amai tare da tsilla gudawa. Da guba irin wannan da ainishin cutar cholera rashin ruwa ke kashe mutum, shiyasa ba abune na juriya dakaji gudawa hade da amai yi maza ka nufi asibiti domin bakasan me zai biyo baya ba.

Allah na tuba shyasa zakuga mutum tun yana iya tashi yaje bandaki da kansa in abun yaci tira sai yakai ga kasa tashi, ko kuma inya mike ya rika tafiya daga-daga zai fadi, saboda electrolytes yai depleating. Wani saide ma ya tare a bandaki, bazai iya dawowa da kafarsa ba.

Sannan ayayin da kake cikin wannan yanayi dehydation din zai sa kidney dinka a mawuyacin hali inda anan ne zaka hadu da Acute kidney injury wanda inba asibiti bane fa komi na iya faruwa, shyasa sam adena wasa da gudawa.

𝐖𝐀 𝐘𝐀𝐅𝐈 𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐅𝐎𝐎𝐃 𝐏𝐎𝐈𝐒𝐎𝐍𝐈𝐍𝐆

Adadin gubar da kaci, shakarunka da kuma yanayin lafiya dama can ajikinka duk suna da tasiri.

  1. Tsoffi: Sunfi hatsari domin kwai ban tausayi idan sukaci guba, domin garkuwar jikin dama ba karfi, ga cuttuka da ciwon jiki da baka rabasu dashi, gashi dama normally karfin kodarsu na raguwa, ko anfara magani basa saurin responding kamar matashi domin komi na jikinsu yai laushi.
  2. Mata masu juna biyu: Saboda ciki akaran kansa yana maida mutum vulnerable ga kwayoyin cuta iri iri domin yana haifarwa da jiki canje-canje don haka in akai rashin sa’a ana iya rasa duk me cikin da abunda ke cikin.
  3. Jarirai da yara kanana yan kasa da shakara 12 suma wannan na daga rukuni mafi hatsari da ba aso guba ta samesu saboda a lokacin garkuwar jikinsu bata riga ta ginu ba.
  4. Mutane masu dauke da cuttuka marasa magani saide management wato irinsu Cancer, cutar kanjamau, ciwon sugar, chemotherapy da sauransu.

Wadannan rukunin mutane 4 din anfi samun mace-mace atsakaninsu insuka sha guba fiye da sauran mutane.

𝐈𝐋𝐋𝐀𝐑 𝐒𝐇𝐀𝐍 𝐆𝐔𝐁𝐀

Zata karar maka da ruwan jiki wanda a dalilin haka zaka iya mutuwa inbaka sami taimakon gaggawa ba.

𝐌𝐀𝐓𝐀𝐊𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐈𝐘𝐀

■ – A tabbatar ana dumama kwanannen abinci, ko kuma wanda ya jima abude ake kokonton ingancinsa.

■- Mutane suke practising abunda muke kira intelligent shopping; wato kada ka shiga kanti ko mall kurum ka fara jidar kayayyaki daka, shyasa zaku ga ko a film ana nuna muku in anje sayayya zakuga turawa sai sun daga abu sun duba gefe da gefe kafin su saka a basket dinsu ko kuma su mayar dashi counter.

Abunda suke dubawa shine ranar da aka buga kayan wato Manufacturing date alamar (MFD) da kuma Expiring date me alamar Best Before (BB). Domin koda bai expire ba inde ya zamto ya cinye kaso 2 cikin 3 na lokacin expire wasu basa dauka. Misali abunda aka bugashi tun October 2018 amma expiring dinsa October 2021. Kaga yaci fiye da shekara 2 cikin 3 wasu bazasu dauka ba inde ya rage kasa da wata 6 yai expire.

■- Kada yi maka arha ko sauki ya rudeka wajen sayayya, domin wasu sun san expire product nema amma suna sane don anmusu arha suke kwasowa, kusani kai aka cuta ko anawa aka baka, kuma inka sayarwa da saura Allah bazai barka ba.

■- Ko ruwan pure water zaka sha duba expiring ko kalarsa dakyau, inbabu ba laifi bane kaqi sayen na kowa sai wanda ka saba sha saboda ka riga kasan kalarsa. Haka kada ka ta6a shan ruwan da leda ko robarsa ke yoyo

■- Idan kunje sayayya musamman madara, kifin gwangwani ko tumatir da sauransu… koda product sabo ne bai expire inde kunga alamun gwangwanin ya lotsa kada ku kuskura ku daukesa koda kuwa ance daga sama mn kanta ya fado ku barsa ko shikenan ku hakura. Wannan na daga matsalolin da ba a daukarsu serious amma illa ne dasu akwai bacteria din da dama wannan damar take jira na gwangwani ya lotsa tana ciki already.

■- Rukunin wadancan mutane 4 masu ciki, tsoffi da yara a kiyaye abunda za’a basu suci kosu shan har sai wanda aka tabbatar da ingancinsa.

■- Ake wanke hannu da kyau, sannan a wanke kayan maramari su ganyayyaki da vegetables da kyau kafin ayanka. Ba laifi bane asa gishiri aruwan wankesu. 🍋🍉🍎🥕🥬🥦🥒🍍🍌

■- A dafa nama ya dahu sosai, babu zancen wai dahuwar nan irin HALF DONE, kuskure ne domin akwai kwayoyin parasites da sai sunji wuta sosai

■- Mahauta da masu sana’ar sayar da sea foods suma su lura da tsaftar guraren sana’oinsu sosai, ake samun musayar iska tare da kore kudaje.

■- A lura da lemukan packet din nan koda da Nafdac number alura dakyau, duk packet din da ya huje ko agaji ana kokonto akai toh kar asha kurum.

■- Magani na iya zama guba don haka aji kuma a kiyaye ka’idar da likita ya tsara na shan magani.

■- Sannan asanar da wanda baisan wannan bayanin ba ya sani shima matakin kariya ne wato yada ilimi atsakanin juna.

𝐌𝐄 𝐘𝐀 𝐊𝐀𝐌𝐀𝐓𝐀 𝐀𝐘𝐈 𝐒𝐀𝐍𝐃𝐀 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌 𝐘𝐀 𝐍𝐔𝐍𝐀 𝐀𝐋𝐀𝐌𝐔𝐍 𝐘𝐀 𝐒𝐇𝐀 𝐆𝐔𝐁𝐀

Inyana tsaka da amai da gudawa ai maza a nemo gishirin ORS ahada abasha akwaso shi zuwa asibiti. Inbabu ORS hada na gishiri da suga local aduramasa ai maza a taho asibiti.

Kul ba’a son shawa gudawa magani don atsai da ita, ko a asibiti bama ba mutum maganin gudawa domin jiki ya riga ya saketa already inkace zaka tsaida ita ka hana cikin motsin da zai fitar da gudawar zaka aikata kisan kai, mutum na iya mutuwa, don haka tsaida gudawar bashine abunda akeso ba, cigaba da bashi ruwan gishiri da sugar shine kurum abunda zakuita yi har akaraso asibiti, ku barshi yaita gudawarsa. Amma kar kubasa komi naci ko sha sai ORS, koda antibiotics ko wani magani karku bashi.

𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐀𝐍𝐀 𝐆𝐖𝐀𝐉𝐈𝐍 𝐆𝐔𝐁𝐀 𝐀 𝐀𝐒𝐈𝐁𝐈𝐓𝐈

Eh likitoci na daukar sample na abunda ake tunanin shi mutum yaci, sannan adau sample na fitsari, amai, gudawa ko jinin mutum atura laboratory ai gwaji domin gano irin gubar da mutum yai arangama da ita.

Sannan ana yin gwajin lafiyar kodar mutum domin tabbatar da larurar taima kidney illa ko kuwa.

𝐌𝐀𝐆𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐌𝐀𝐓𝐒𝐀𝐋𝐀𝐑

Wannan aikin manyan likitoci ne, matakin farko shine likitoci zasui kokarin mayarwa da mutum electrolytes din da ya rasa har sai gudawar ta tsaya don kanta, daga nan idan kuma mara lafiya yana bukatar jini zasu nemi akawo jini matsayin emegency action.. kafin daga bisani su bi sauran complications din su magancesu.

𝐑𝐈𝐒𝐄 𝐀𝐋𝐀𝐑𝐌

A duk sanda aka sami mutum sama da 4 na fama da zazzabi, amai da gudawa da ake tunanin cholera ko shan wani abune, ai hanzarin sanar da jami’an lafiya su kuma su sanar da ofishin kula da lafiya na karamar hukuma domin daukar matakin da ya dace.

Shyasa zakuga nasa sticker ambulance asama 🚑 alamun emergency situation, rasa rai kamar wasa ne zakaji ana mutu in aka tsaya wasa. Sannan kuke bawa hoton da nake sawa a kasan post mahimmanci suma akwai sakon da suke isarwa ba kurum ina sasu ne don ina sonsu ba.

Allah ya tsare mu.

☆☆☆
(𝐈𝐛𝐫𝐚𝐡𝐢𝐦 𝐘. 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button