Girki Adon UwargidaHoto Mai MaganaIslamic ChemistLABARAI/NEWS

LARURAR MINSHARI [SLEEP APNOEA]

LARURAR MINSHARI [SLEEP APNOEA]

Munshari matsala ce mai girman gaske da wadansu da dama suke zaton ba larura bane.

Mutane da dama su kanyi fama da matsalar ne yayin barci. Galibi basa sani saide in ance sunayi su rika mamaki. Toh amma akwai lokutan da asu kansu sukan iya tuna cewa kamar numfashi baya isarsu yayin bacci, har sukan rika farkowa. Yakan faru ga kowa amma de anfi ganinsa a mutane masu kiba sai kuma wadanda inka duba bakinsu zakaga Tonsils dinsu 6alo-6alo ba a iya hango bellu dinsu.

Kai akwai mutanen ma da saboda mummunar kiba (obesity), idan kazo kusa dasu ko ba barci suke ba zaka jisu kamar masu minshari, wato zakaji numfashinsu kara yake koma gurnani. Wannan ba karamin hatsari bane ga lafiya musamman zuciya da kuma kwakwalwar mutum domin suna mawuyacin yanayi.

Tabbas da dama a dabi’ance kamar yadda na fada da yawa basa sanin sunayi, sai wani na kusa dasu musamman abokin kwanansa, ko mahaifiyarta ya fara korafi.

Hasali ma anfi samun wannan korafi a tsakanin ma’aurata, kuma yakan iya jefa aure cikin hadari, musamman ma idan daya yanayi, daya kuma baya yi.

Akan iya samun matsalarma a tsakanin ’yan uwa masu kwana a daki daya. Duk da cewa kowane irin dan Adam kanyi minshari a barci jefi-jefi kuma bamai kara sosai ba, amma dai ana ganin wannan matsala ta minshari mai nauyi, wadda zata iya ta6a lafiyar zuciya tafi yawa a mutane masu kiba (obese people) mace ce ko namiji kamar yadda na fada. Kai har a motar haya wani bun inbacci ya kwashe mutum haka zakaji yana yinsa gwanin ban al’ajabi.

Kai wasu lokutan ma matsalar tafi kamari a yara masu kiba. An kiyasta cewa fiye da rabin mutane masu kiba suna fama da wannan larura. Banda masu kiba kuma mutanen da suka fi sauran al’umma minshari sune mashayan taba sigari.

MEKE HADDASA HAKAN

Minshari kan faru ta sanadin abubuwa da dama kamar;

1- karkarwar tantanin makwallato a lokacin barci (laryngomalacia)

2- Yawan zukar taba sigari wanda hakan nasa nan ma wannan tantanin na murya ya sakwarkwace, ko

3- Rashin wucewar iska zuwa huhu kai tsaye (a wadanda kiba tayi yawa kenan a jikinsu da wuyansu) saboda kitse.

4- Kumburin tonsils na gefe da gefen hank’a…

5- Cutukan huhu; irinsu limoniya, tarin tb da sauransu

6- Sai kuma kwanciya ba daidai ba (poor positioning) ta yadda harshen mutum ko k’ashin mukamiki kan toshe hanyar numfashin.

🎫🎫🎫🎫
Yayin wannan alamari numfashi yakan rika daukewa na wani lokaci wanda hakan kan iyasa mutum ya wuce acikin bacci saide ace lfy aka kwanta dashi amma anwayi gari da rasuwarsa!saboda daukewar numfashin ya jefa kwakwalwa cikin karancin iska Wanda Hypoxia din ita je kashesu

Ko kuma da yawa hakan yasa su rika yawan tashi cikin barci. Wanda wannan yawan farkowar kansa mutum yawan barcin rana da kasala a yayin aiki.

Babban hadarin dai da irin wannan matsala kan kawo itace idan mutum na minshari kuma numfashi yana daukewa kuma ya kasa tashi ko juyi domin iska ta shiga to hakan na jawo yiwuwar hatsarin bugun zuciya cikin barci wanda wannan ma na daga abunda kesa mutum ya mutu cikin barci.

Kamar yadda nace wannan na faruwa ne saboda idan huhu ya dade babu iskar oxygen (inspirational reserved volume) a cikinsa zuciyace ke fara ganewa ta hanyar jinin data dauko daga huhun. Idan jinin ba iskar oxygen a cikinsa (oxygenated blood) iskar da itama kanta zuciyar ta ta’allaka akai wajen aikin buga jini zuwa sauran sassan jiki sai yasa bugun zuciya ya dan samu tangarda, wanda shi ake kira bugun zuciya.

Duk da cewa dai a lokuta da dama zuciyar na farfadowa da kanta bayan an samu bugun zuciya, idan ba’a rage kiba ba, tabbas matsalar ba sauki zata yi ba. Wannan na daya daga cikin manyan abubuwan dakan jawo akance mutum ya cika a cikin barci. Ko kuma akwanta lfy da mutum awayi gari bashi.

MATAKAN DA MASU MINSHARI DA KIBA ZASU DAUKA

1]- Rage kiba ta hanyar yawan motsa jiki akalla minti 30 kullum tsawon kwanaki 5 asati koma kullum kullum kurum

2]- Sai kaucewa cin abinci lokacin da mutum baya jin yunwa tare da cin kadan daidai misali yayin jin yunwar. Kar mutum yake take cikinsa da abinci.

3]- Rage maiko a abincin, daina cin su chocolates da junk foods tare da maye gurbinsu da ganyayyaki (vegetables & fruits) a abincin shine mafita.

4]- Yawanci mutane da yawa suna tambayar magani wai ganinsu rage kiba sai dai ta hanyar kwayoyi. Wannan kansa makogwaron da kiba ta matse ya dan bude muryar mutum ta lalace

5]. Sai kuma kiyaye yanayin kwanciya, wato banda sa pillow, banda sa zanin gado me laushi… banda tayar dakai da kowanne irin abu.

Sannan banda kwanciyar rigingine ta GADON BAYA fuska na kallon sama…… Domin Kwanciya ta gadon baya SHI kesa HARSHE ya fadawa makogwaro ya toshe hanyar numfashi, don haka dole a kula da kwanciya da gefen jiki kawai. Banda kuma kwanciyar ruf da ciki

6]. Wata hanyar kiyaye karkarwar tantanin makwallato kuma itace ta barin shan sigari ga masu sha.

🎫🎫🎫
Wanda kuma ya dauki duk wadancan matakai, amma munsharinsa yaki tafiya, wajibi yazo yaga likita akwai ’yan dabaru da akan yi a asibiti na gyara yanayin tantanin ko na makogwaron. Bayan likita ya kashe makogwaron da abin fesawa na kashe zafi (regional anaesthesia) akanyi allura, ko amfani da hasken wutar laser a rage abinda yake toshe makogwaron.

Likitocin ENT (OTOLARYNGOLOGIST) su ya kamata mutum yaje ya gani… yawanci ana iya samun ganinsu kai-tsaye a kankanen lokaci tunda marasa lfy basu cika yi musu yawa ba.

Wanda a al’adance, wannan na daya daga cikin dalilan da kansa ana yankewa yara belu tun suna jarirai, duk da cewa shima akwai illolin dake tattare da hakan. Domin ko ba acire belu ba ba abunda zai samu yaro toh amma idan ya zamto jariri na munshari ko yawan farkowa ta ba laifi bane acireta… akwai bukatar yi masa din.

[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button