FadakarwaIslamic Chemist

LIKITA NI KUMA CIWON ƘAFAFU DA HANNUWA KE DAMUNA, NAJE HAR ASIBITI

LIKITA NI KUMA CIWON ƘAFAFU DA HANNUWA KE DAMUNA, NAJE HAR ASIBITI


Naje har asibiti anbani Magani ya ɗan yi sauki toh amma yanzu sai naga kafafuwan nawa suna dan kumburi har da lotsawa ina dannasu. Shine nake neman shawara ???

AMSA:

A lokuta da dama mutum zaije asibiti sau ɗaya tak aji irin korafinsa a bashi magani kawai batare da anyi masa wasu gwaje-gwaje ba. Wannan takan faru kuma ba laifi akayi ba.

Amma idan mutum yayi amfani da magani kwana daya, kwana biyu zuwa uku ba canji, koh aga abu yazo ya wuce nada tsanani, anan mutum ai shima yasan dole ya koma asibiti. A wannan zuwa na biyu mafi yawan likitoci ko masu jinya zasu ɗan kara bincikar mutum ta hanyar aune-aune da gwaje-gwaje, duk da cewa anfiso ayisu tun zuwan farkon.

A wasu lokuta zan iya cewa a gaskiya tunanin ɗorawa mara lafiya nauyi biyu: Na kudin gwaji dana sayen magani ke hana wasu ma’aikatan rubuta duka abubuwan da suka dace, sbaoda wasu marasa lafiyan daga tambayoyi zaka fahimci irin rayuwar da suke ciki, wasu tun agabanka suke fara kuka saboda tsananin rayuwa.

☆☆☆
To amma de dangane da tambayarka mu a kimiyyance kumburin hannu ko kafa mai lotsawa ciki in andanna anfi danganta shi da taruwar ruwa karkashin fata (edema). Wanda kan faru koh dai idan wani abu ya taɓa Hanta (LIVER) ko ƙoda (Kidney) ko Zuciya (Heart).

Babbar matsala ko karamar ƴar tangardar dukkansu sukan iya sa maka wadannan alamu amma a likitance mukan bambance na;

■ Ƙoda (kidney dx) da cewa kumburin yafi yawa a fuska musamman da safe,

■ Na tangarɗar zuciya (Heart dx) yafi yawa a ƙafa zuwa hannuwa. Saide anan a Mata masu juna biyu wasu lokutan karancin jini kan haifar musu da hakan. Amma de inbabu ciki, kuma kamar da kake namiji toh duk abun daya ne. Sai kuma….

■ Na hanta (liver disease) kuma yafi yawa a wajajen ciki wanda mukan kira da ascites.

Duk da wannan baki ďaya hasashe ne bisa ilimin da Allah ya horemana da kuma ganin na’uikan marasa lafiya iri-iri masu matsalolin, Amma duk da haka sai anyi aune-aune da gwaje-gwaje ake tabbatarwa.

Don haka shawara anan itace kai dama duk me matsala makamancin wannan dake saurarena akoma asibiti, koma ka tafi babban asibiti idan ada karami kaje, ka samu a sake ganinka.

Idan basu rubuta maka gwaje-gwaje ba ka bukaci hakan da kanka, ko yaushe mara lafiya na iya neman gwaji koda likita baibasa ba inyasan zai iya yi.

Wannan shine.

[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button