LABARAI/NEWS

MABIYA ADDININ KIRISTANCI NA DUNIYA NA FUSKANTAR BARAZANA

MABIYA ADDININ KIRISTANCI NA DUNIYA NA FUSKANTAR BARAZANA
Hankalin Fafaroma Ya Tashi Sakamakon Gano Wani Bible Da ‘Jesus’
Ke Wasiyyan Zuwan Annabi Muhammadu (S.A.W)
‘Yan sanda a kasar Turkiyya sun gano wani tsohon littafin bible
wanda ake kyautata zaton a cikinsa akwai inda, Annabi Isah A.S
(Jesus) ya yi wa mabiyansa albishir da zuwan Annabin karshe mai
suna Muhammad (Annabi Muhammadu S.A.W).
An yi ittifakin cewa Littafin ya kai shekara 1,500 da rubutawa. Kuma
an rubuta shi ne da ruwan zinari a cikin harshen “Aramaic” (Larabci).
Jaridar Daily Mail ta Amerika ta ruwaito cewa, gano littafin wanda
aka yi hasashen duk falle daya a cikinsa zai kai kimanin Yuro milyan
£14 ya jawo muhawara mai tsanani a tsakanin mabiya darikar Vatican
da musulmi inda har Fafaroma Pope Benedict XVI ya nemi a kawo
masa bibile din ya gani.
Idan dai aka tabbatar da zargin da ake yi akan Bible din kuma ta
tabbata haka din ne. To akwai chakwakiya ganin cewa littafin zai
karyata mabiya addinin kirista dake Allantar da Isah (AS) da kuma
masu cewa Jesus din dan Allah ne. Bible din zai tabbatar da cewa
addinin Islama shine gaskiya kuma Musulmai sune ke kan addini na
gaskiya wanda (Almasihu/Jesus) ya umurci mabiyansa akai.
Majiyar ta mu ta kuma ruwaito cewa an gano littafin ne tun a
shekara ta 2000 amma hukumomin kasar Turkiyya suka cigaba da
tsaron shi har zuwa shekara ta 2012 inda suka kaishi gidan tarihi na
Ankara Ethnography Museum. Kuma ana sa ran nan bada jimawa ba
za’a rika nunawa mutane Bible din a gidan tarihin kasar.
Ministan raya Al’adu da yawon bude ido na kasar Turkiyya, Ertugrul
Gunay ya ce suna kyautata zaton Bible din na gaskiya ne shi yasa
wasu suka boye shi saboda yadda littafin ya yi bayani akan ainihin
matsyin Almasihu (Jesus) sabanin tunaninsu.
Jaridar ta daily mail ta kara da cewa hankalin fafaroma da sauran
manyan limaman kiristoci ya tashi sakamakon gano wannan littafi na
Bible.
Don Allah idan ka karanta ka tura a other groups.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button