LABARAI/NEWS

MAFI MUNIN TARIHI DA ZALUNCIN FARANSA GA MUSULMI

MAFI MUNIN TARIHI DA ZALUNCIN FARANSA GA MUSULMI

Kasar France ta tara malamai musulmi guda 400, suka yanke kawunansu da adduna; A lokacin mamayar kasar Chadi a shekara ta 1917 miladiyya

Lokacin da Faransa ta shiga birnin Laghouat na Aljeriya a shekara ta 1852 AD, ta halaka kashi biyu bisa uku na al’ummarta… ta hanyar kona su da wuta, kuma duk a cikin dare daya

Faransa ta gudanar da gwaje-gwajen Nukiliya har sau 17 a kasar Aljeriya a tsakanin shekarar 1960 zuwa 1966, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 27 zuwa dubu 100 da ba a bayyana tabbacin adadinsu ba.

Lokacin da Faransa ta bar Aljeriya a shekara ta 1962, ta buda ma’adanai fiye da na al’ummar kasar ta Aljeriya a lokacin sunada ma’adanai miliyan 11 karkashinsu.

Faransa ta mamaye Aljeriya tsawon shekaru 132. Faransawa sun mamaye musulmi miliyan daya a cikin shekaru 7 na farkon zuwansu, kuma miliyan daya da rabi a cikin shekaru 7 kafin tafiyarsu.

Wani masanin tarihin kasar Faransa Jacques Gorky ya kiyasta cewa adadin wadanda Faransa ta kashe a kasar Aljeriya, daga zuwanta a shekara ta 1830 har zuwa tafiyarta a shekara ta 1962 sun haura musulmi miliyan 10.

Faransa ta mamaye Tunisia tsawon shekaru 75, Algeria shekaru 132, Maroko shekaru 44, da Mauritania shekaru 60.

A lokacin da Faransa ta shiga Masar a yakin da take yi, sojojin Faransa sun shiga masallatai da dawakansu, inda suka rika yi wa mata fyade a gaban iyalansu.

Kuma sun sha barasa a cikin masallatai, kuma sun mayar da masallatai da dama matsugunin dawakansu.

A karshe saboda zalunci da karya sun ce Musulunci addinin ta’addanci ne, kuma Annabinmu Annabin ta’addanci ne

Wani abin mamaki sai ka ga wasu suna ta baje kolin wayewar kasar Faransa har ma suna kare ta suna mantawa da bakaken tarihinta.

Wannan ita ce Faransa.

Repost Daga: @Skipper Editing: Bieen Basheer

Allah ya ruguza makiya Musulunci da Musulmai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button