Latest Hausa Novels

MAFITA GA DALIBAN JAMI’A KAN YAJIN AIKIN KUNGIYAR (ASUU) 2022

MAFITA GA DALIBAN JAMI’A KAN YAJIN AIKIN KUNGIYAR (ASUU)..

A daren jiya ne bayan kanmala Mitin da aka kwashe kusan awwani goma sha biyar tsakanin wakilan ASUU da FG neman daidaito kan janye yajin aiki na gargadi da akaje na tsawon sati shida. A karshe dai tattaunawar bata haifar da tsamai ido ba, ita kunginyar ta ASSU ta kara tsawaita wa’adin yajin aikin har zuwa sati takwas.

In kana bibiyar lamarin da bu’de’dden zucciya, a iya cewa cikin wannan rigimar ASUU tafi kusa da gaskiya, duk da abunda suke fafutuka akai mafi yawa daga ciki bu’katunsu ne, Amma zai taimaki Dalibai ta wani bangaren.

Kuma ya kamata mu sani da dama cikin wannan bangarorin biyu, ‘ya’yansu basa karatu a kasar nan, Majority of them suna kasashen turawa, wasunsu kuma na Makarantun Private na makudan kudi a nan gida Nijeriya, shiyasa zaku ga ana ta hasko hotunansu a wajen gradution din ‘ya’yan nasu a kasar waje, hakan yasa suka kasa daukan mataki akan wannan matsala ta yajin aikin Malaman Jami’o’in Gwamnati, inda ‘ya’yan talakawa zasu ce sun fasa karatun, wallahi zasuji dadi dama abunda suke bukata kenan.

Ina ‘yan uwana da wannan abun ya shafa, ya kamata muyiwa kanmu karatun ta natsu, babu inda kukayi alkawari da Ubangiji lallai sai kayi karatun boko kafin kayi arziki, domin sanin kanmu ne a kasar nan akwai attajirai hamshakan masu kudi da basu karatun boko ba, amma dayawa daga cikin masu Doktoci, Mastoci a karkashin kamfani ko ma’aikatansu suke aiki, kuma su ke biyansu albashi, wannan ya ishemu misali..

MAFITA GA DALIBAN JAMI’A KAN YAJIN AIKIN KUNGIYAR (ASUU) 2022

A nan shawarata garemu itace, a cikin mu akwai masu sana’a, toh lallai mu rike sana’ar nan komin kankantar ta kar mu raina sana’ar mu, sannan wadanda basu da sana’a su nemi sana’ar yi ko da kuwa leburanci ne, hakan zai taimaka mana wajen tsayuwa da kafafunmu, in Allah ya sanyawa sana’ar Albarka sai asha mamaki yadda labari zai canza. Kai za’a iya kai lokacin dama in su FG sun kasa biyan ASUU hakkinsu, toh a cikin mu albarkar sana’ar nan zamu zauna da Kungiyar ASUU mu biya musu bukatunsu, su dawo su cigaba mana da karatu don masalahar talakawa..

Ina Iyayenmu Mata, kar ku yarda matsalar yajin aikin ASUU ya hanaku zuwa gidajen auranku, shi aure baya hana karatu, in kin duba a ajinku zakiga akwai Matar Aure, don haka mutuncinku kenan gidan Mazajen Aurenku.

Allah ya kawowa talakawan Nijeriya mafita, Dalibanmu Allah ya kara muku hakuri, Allah ya zaunar da kasar lafiya. Amin.

Sa’eed Usman Dakingari,
Dalibi Daga: Jami’ar Maitama Sule,
Univeraity, Kano..
14/March/2022..

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button