LABARAI/NEWS

Maganar Kai Hari Abuja Labarin Kanzon Kurege Ne ~ Cewar Sufetan Yan Sandan Ƙasa

Maganar Kai Hari Abuja Labarin Kanzon Kurege Ne ~ Cewar Sufetan Yan Sandan Ƙasa

Babban sufeton yan sandan kasar nan Usman Alkali Baba, ya sake yin watsi da rahoton dake cewa akwai yiwuwar kai hari birnin tarayyar Abuja.

Ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin da yake jawabi a hedikwatar rundunar yan sandan jihar Delta, inda ya bayyana rahoton a matsayin labarin karya.

Idan za a iya tunawa a Lahadin data gabata, kasar Amurika da Burtaniya sun yi gargadin cewa, akwai yiwuwar samun harin ta’addanci a birnin tarayya, wanda kuma zai shafi gine ginen gwamnati da wuraren ibada, tare da makarantu da kuma wuraren taruwar jama’a.

Yayin daya amince cewa akwai alamun rashin tsaro, babban sufeton ya dora alhakin haka kan kasar Amurika, bisa kin bada bayanan sirri ga hukumomin tsaron kasar nan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button