LABARAI/NEWS

Mahaifiya a garin Zariya tayi Shelan Neman Wanda zai Kashe mata Dan da ta haifa

Mahaifiya a garin Zariya tayi Shelan Neman Wanda zai Kashe mata Dan da ta haifa

Wata mahaifiya a garin Zariya Jihar Kaduna ta Shaidawa Jami’an tsaro na Yan Sanda Shiyyan Zariya cewa da Allah Zai kawo Wani mutum dan albarka da zai Zama Silar mutuwar Dan cikinta da Sai ta kwana tana Masa addu’ar Allah ya biya shi ita a nufinta akashe kawai kota halin Kaka Saboda yafi karfinta kullum shikenan hadata rigima da al’umman gari

Usman Shine Sunan Matashin Wanda mahaifiyarsa ta gaji da ganinsa a doron Kasa Saboda irin rigimar da yake dauko Mata yau Shine ya Sari wancan gobe ya Soke wancan

 

 

Hakan ya Kara bude Wani Sabon fai-faine a dalilin yadda Matashin ya Sossoki Wani Dan uwansa Matashin Mai kimanin Shekara 29 da wuka har sai da lamarin ya Kai ga Yan Sanda Inda aka bukaci mahaifiyar Wanda ya aikata wannan mummunar ta’asar data bayyana a gaban hukuma duba ga yadda Shi Dan nata yayi na Kare

 

mahaifiyar Usman din tayi gaban Yan Sanda Mahaifiyar ta Cigaba da Shaidawa Jami’an tsaro ita Bata San inda Dan nata ya shiga ba amsar da ta baiwa Jami’an tsaron kenan bayan tambayarta da Jami’an tsaron Suka Yi Shin ko ta San inda dan nata ya Shiga Bisani yadda Jami’an tsaron ke sintirin farautar Usman din a domin ya gurfana gaban hukuma Kan irin ta’asar da yayi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button