LABARAI/NEWS

Makarantun mata zalla na jihar Bauchi sun fara aiki duk da zanga-zangar dalibai maza

Makarantun mata zalla na jihar Bauchi sun fara aiki duk da zanga-zangar dalibai maza

Gwamnatin jihar Bauchi ta kaddamar da shirinta na makarantun zalla duk da adawar da shirin ya fuskanta daga dalibai maza a jihar.

Kwamishinan ilmi na jihar Bauchi, Dr. Aliyu Tilde ya bayyana a wata sanarwa da ya wallafa cewa an fara sabon tsarin ne ranar Litinin a makarantun da ke garuruwa daban-daban a jihar.

Ya ce za su yi aiki kan sabon tsarin ne a matakin gwaji, kuma a shirye gwamnati take ta karbi korafe-korafe daga iyaye da dalibai.

A farkon makon nan ne aka ga hotunan wasu dalibai maza da rahotanni suka ce daliban makarantun sakandire ne da ke gudanar da zanga-zanga don nuna adawa da tsarin raba mata da maza a makarantu.

Dr. Aliyu Tilde ya ce sun lura da yamadidi da karin gishirin da masu adawa da shirin suka rika yi “don wasu yara kamar 50 daga makarantu biyu a garin Bauchi sun yi zanga zanga game da shi A cewarsa da ma duk tsari mai kyau ba ya rasa kalubale ko mai kyawunsa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button