ylliX - Online Advertising Network Makauniyar Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar sarauniyar Kyau Ta Jihar Rivers - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Makauniyar Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar sarauniyar Kyau Ta Jihar Rivers

Makauniyar Da Ta Zo Ta Biyu A Gasar sarauniyar Kyau Ta Jihar Rivers

Wata ƴar Najeriya mai tallan kayan ƙawa Favour Rufus, da aka gano tana da ciwon makanta tun tana shekara bakwai, ta ce har yanzu tana da burin zama sarauniyar kyau.

A baya-bayan nan ne Favour ta fafata da mutum 18 a gasar sarauniyar kyau ta birnin Fatakwal wato Miss Port Harcourt City, wadda ita ce gasa mafi girma ta jiha a Najeriya.

Inda ta zo ta biyu a Mutane da dama ba su ba ni ƙwarin gwiwa ba. Da yawa ma dangina ne kamar yadda Ta ce malamanta ne suka fara gane cewa tana da matsalar idanu bayan da suka lura ta daina ƙoƙari a aji

Da aka je asibitin ido sai aka tabbatar mata da labarin mafi muni
Likitan idon ya gaya min cewa an makara. Na rasa idona na hagu Amma an ce mata idonta na dama lafiyarsa ƙalau, kuma dole sai ta dinga ɗiga maganin ciwon ido.

Favour ta ce a lokacin ma dishi-dishi take gani da idanun nata, kuma ta dogara ne da horon da ta samu daga wajen horaswa
Duk da ƙalubalen da take fuskanta, ta ce ba za ta karaya ba wajen cimma burinta na zama sarauniyar kyau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button