LABARAI/NEWS

Malamin Islamiyya Ya Fada Tarko Bisa Mu’amala Da Matar Aure

Malamin Islamiyya Ya Fada Tarko Bisa Mu’amala Da Matar Aure

An tsare wani malamin Islamiyya, bisa zargin yin huldar da ba ta dace ba, da dalibarsa wadda take matar aure ce, kuma take zaune a gidansa fiye da wata daya, ba tare da sanin mijinta ba, bisa umarnin mai shari’a Khadi Abdullahi Nasiru na kotun Shari’a da ke Minna, ta jihar Neja.

Haka kuma ana zargin malamain da zubar da cikin matar auren, ya kuma ba ta maganin samun tazarar haihuwa.

An ce malamin ya boye matar ce wadda ke da ‘ya’ya biyar a gidansa kusan tsawon kwana talatin da biyar ba tare da ta leka gida ba, bayan tashi daga makarantar islamiyyar.

Lokacin da alkali ke sauraren karar, wanda ake zargin ya ce wa kotu matar ce ta kawo masa koke a kan mijinta cewa, ba ya kula da ita.

Da suke musanta maganar da malamin ya yi ‘yan uwan matar sun gaya wa alkali cewa ‘yarsu ta koka kan cewa, tsawon shekara goma sha uku da yin aurensu mijin bai san ya ba ta abinci ba. Ba a samu fahimtar juna ba tsakanin malamin da mijin wannan mata ba, wanda ya gaya wa malamin cewa, matar ta sa na da aljanu da za su warware zare da abawa.

An ce, sakamakon haka, sai malamin makarantar ya bukaci matar ta zo ta zauna a gidansa, suka kuma ci gaba da hulda ta kud-da-kud.

Loacin da Khadi Nasiru ta gaya wa wanda ake zargin cewa, yanzu haka binciken da kotu ta yi ya nuna cewa, an kama matar da kwayoyin da mata ke amfani da su don samun tazarar haihuwa, kuma ya amsa cewa shi ya ba ta, amma ya nemi a yafe masa.

Ya ci gaba da cewa, an zubar da cikin saboda umarnin da aljanin da ke jikin matar ya bayar na dakatar da mijin daga azabtar da ita,”aljanin ya ce, mijin na son kashe ta”.

Haka kuma, lokacin da take magana, matar ta zargi malamin da hada kai da matarsa dokin su lalata rayuwarta, yayin da take gaya wa kotu cewa, ba ta san cewa ba a gidan mijinta take ba,iya tsawon zaman da ta yi.

Bayan sauraren kowane bangare mai shari’a Khadi Nasiru, ya dage sauraren karar zuwa ranar 17, ga watan Mayi 2022.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button