LABARAI/NEWS

Mallamin karshen duniya!

Mallamin karshen duniya!

Wannan mutumin da kuke gani mai suna Yahya Isah Mai mata daya da yara uku, wanda ake wa lakabi da Mallam Yahya Isah yana zaune a unguwan dake bayan Flamingo, Maitumbi Minna. Yana koyarwa a wani Islamiya mai suna Rashadiya, a bayan Flamingo. Yayha da kuke gani babu abunda yasa a gaba sai niman matan aure.

Kwanakin baya azumi na biyar, wata matan aure wanda ta kasan ce daliba ga Yahya mai yara hudu ta bata. Yan uwan ta da mijin ta suka bazama Neman ta. Har ya kai su Yan uwantan suka kira shi a waya suka sanar da shi batar ta. Har yaje gun maman matan da ta bata ya jajanta mata. Ya Kuma ce zai saka ta cikin addu’a insha’Allahu za’a gan ta.

Bayan an kwan biyu dab da sallah karama, sai Yan uwan matan da ta bace suka sake kiran Mallam Yahyan a waya suka ce masa har yanzu dai ba’a samu labarin ta ba. Sai yace musu insha Allah bayan sallah zata dawo, Yana kan addu’a ma yanzu haka. Sai iyayen suka masa godiya suka ce Allah Ya kai rai da lafiya.

Bayan anyi sallah har da sati daya sai Yan uwan suka samu labarin an gan ta a wani wuri amma da suka je ba su same ta ba. Bayan kwanaki uku da yin hakan, sai shi mijin matar da ta bace ya kirayi Yan uwan ta yake ce masu shifa yana zargin Mallam Yahya kan batar matar sa don yanzu haka yaje unguwan shi Mallam Yahyan, yana haduwa da yarinyar mallam Yahyan sai ta fece da gudu ta yi gida. Ba’a jima ba sai Mallam Yahyan ya kirayi shi mijin matar da ta bace a waya yake ce masa kana zargi na da batar matar ka koh? Sai yace subhanallah. Haba Mallam, ya zan zarge ka da wannan mummunan abun? Wallahi ko kadan bana zargin ka. Sai Mallam yace masa to mai ya kawo ka unguwa na kai da kake bosso? Sai yace masa yazo ganin wani abokin sa ne, Kuma daga nan kasuwan kauye zai je.

Sai suka ce ya masu kwatancen gida mallamin, sai yayi masu. Sai suka taso suka zo har gidan Mallam Yahyan sukayi sallama sai matar sa ta fito. Sai suka ce nan ne gidan Mallam Yahya? Sai tace eh. Sai suka ce don Allah a kira masu shi. Tana kama hanya zuwa wurin kiran sa, sai ita yayan matar da ta bace ta bita a baya. Ita matar Mallam Yahyan na shiga dakin sa, sai yayan matar da ta bace ta apka dakin, kawai sai ga Yar uwan ta da Mallam Yahyan daga ita sai zani a kirji. Nan take ta saka ihu sauran Yan uwa suka shigo suka ganewa idanun su.

Sai suka dauki shi Mallam Yahyan da ita matar auren zuwa gidan Sarkin Minna. Daga gidan sarkin Minna, aka turo su zuwa kotun bola dake unguwan Sarkin Minna. Yanzu haka ana nan kotu da shi Mallam Yahyan da ita matar da ta bace da Yan uwar nata. Ance har manya sun fara kiran alkalin kan a saki shi Mallam Yahyan, babu ruwan su da matar da aka zalunta.

TSUFA YAYI GARDAMA: An kama Kaka Da Jikanta Suna Lalata.
.
.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button