LABARAI/NEWS

MANYAN ANGUWANNI MASU TSOHON TARIHI A CIKIN BIREIN ZARIYA 

MANYAN ANGUWANNI MASU TSOHON TARIHI A CIKIN BIREIN ZARIYA 

MANYAN ANGUWANNI MASU TSOHON TARIHI A CIKIN BIREIN ZARIYA

.

HOTO: Wannan hoton wani yanki ne na cikin birnin zaria, Titin bayan gidan sarki , titin da zai fitar dakai har hanyar jos , wajen duten Madarkaci dake bakin titi.

.

Manyan Anguwanni a zariya. Mafi yawancin su sun sami sunansu ne daga sunan wasu mazajen da ada aka yi a Anguwar,kuma akasarin wadannan Anguwanni suna cikin Birnin zariya ne kuma suna da masu kulawa da su, wato masu Anguwan. Hudu daga cikin wadannan Anguwanni nan ne ake da gidajen sarautar da muke da su a cikin zazzau. Wato kamar:-

.

1. KWARBAI:- Nan ne Jinsin Mallawa suke zaune.

2. KAURA:- Nan ne Jinsin Barebari suke zaune.

3. RIMIN TSIWA:- Nan ne Jinsin Katsinawa su ke zaune.

4. ANGUWAR BISHAR:- Nan ne Jinsin Sullubawa suke.

.

GA TSARIN ANGUWANNIN DAKI-DAKI

.

1. Kwarbai

2. Kaura

3.. Rimin tsiwa

4. Anguwar Juma

5. Durumin Jamo

6. Durumin mai Garke

7. Limancin kona

8. Limancin iya

9. Kusfa

10. Kakaki

11. Anguwar Katuka

12. Anguwan Alkali

13. Anguwar bishar

14. Anguwar Magajiya

15. Anguwar makama Dodo

16. Anguwar zakara

17. Anguwar zariya

18. Anguwan liman

19. Anguwan Magajin Aska

20. Anguwan lemu

21. Anguwar Jamawa

22. Anguwan Mele

23. Anguwar Dan jinjiri

24. Anguwan Doya

25. Anguwan Malam sule

26. Anguwan Fatika

27. Anguwan Kilu

28. Anguwar Fulani

29. Anguwan Kahu

30. Anguwar Madaka

31. Anguwar Dan Madami

32. Anguwar Iya

33. Anguwar Taba

34. Anguwar Nufawa

35. Anguwar sirdi

36. Iyan Juma

37. Kofar kibo

38. Jushi

39. Ban zazzau

40. Fan Madauci

41. Fan wanki

42. Zage zagi

43. Kan Tudu

44. Rimin Bindiga

45. Fadi sonka

46. Kurna

47. ‘yan Tukwane

48. Bakin kasuwa

49. Marmara

50. Kofar Doka

51. Jakara

52. Kwangero

53. Kwanna Malla

53. Kofar kibo

54. Albarkawa

55. Rimin Danza

56. Rimin Kambari

57. Rimin doko

58. Babban Dodo

59. Anguwan Rubu

60. Kofar gayan

61. Kofar kona

62. Kofar kuyambana

63. Magajiya

64. Kwankira

65. Rimin Danza

66. Anguwan Fatika

67. Anguwan Malamai

68. Anguwan Kahu

69. Anguwan Amaru

70. Madarkace

71. Anguwan Bambale

72. Anguwan Karfe

73. Kamfage

.

Wadannan Anguwanni yawancinsu suna karkashin anguwa guda ne, sai dai saboda yawa aka yi musu lakabi ta yadda za’a gane wurin. Irin wannan lakabi ya danganta da irin sana’a ta wurin ko kuma wani mashahurin mutum da ke zaune a wurin, ko kuma wani abu da aka yi a wurin, shi ya sa aka samu wasu sabbin anguwanni . Misali kamar Anguwannin da suke karkashin Kwarbai sune Anguwar Doya, Anguwar katuka, kantudu, Jamawa, Magajiya. Hakama kuma akwai wadanda suke karkashin kaura , suna kamar Rimin Doko, Rimin Kambari, Kwankira da Fan Madauci. Haka kuma akwai wadanda suke karkashin Rimin Tsiwa, kamar Kwangero, Anguwan Dan Madami, lemu, Rimin Kwakwa.

.

A takaice dai wasu anguwanni suna karkashin wasu ne. Saboda yawa da akayi aka rarraba su.

.

KA/KIN GA SUNAN ANGUWAN KA/KI A NAN?

.

KO AKWAI ANGUWAN DA MUKA MANTA BAMU FADA BA?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button