ylliX - Online Advertising Network Manyan Ayyukan Alkhairan Buhari Da 'Yan Najeriya Za Su Dinga Tunawa Dashi Bayan Ya Sauka Daga Mulki - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Manyan Ayyukan Alkhairan Buhari Da ‘Yan Najeriya Za Su Dinga Tunawa Dashi Bayan Ya Sauka Daga Mulki

Manyan Ayyukan Alkhairan Buhari Da ‘Yan Najeriya Za Su Dinga Tunawa Dashi Bayan Ya Sauka Daga Mulki

Bayan Buhari ya sauka daga mulki zakaji ana cewa;

 1. Shine ya ida ginin Second Niger Bridge.
 2. Shine ya sake Gina hanyar Abuja-Kaduna-Kano.
 3. Shine ya Gina Layin Jirgi na Ibadan zuwa Lagos.
 4. Shine ya Gina Layin Jirgi na Itakpe zuwa Warri.
 5. Shine ya sake Gina hanyar Kano-Maiduguri.
 6. Lokacinsa ne muka fara ganin shinkafa yar gida a cikin buhu kamar yar waje.
 7. Lokacinsa ne aka fi samun wutar lantarki tunda aka dawo mulkin dimokradiyya.
 8. Shine ya Gina Layin Jirgi daga Kano-Kazaure-Katsina-Maradi.
 9. Shine ya Sanya bututun iskar gas tun daga Kogi har Kano.
 10. Shine ya ida ginin hanyar Kano-Katsina ya kuma mai data hannu biyu.
 11. Shine ya ida aikin ruwan sha na zobe Dam, daga Dutsinma zuwa Katsina.
 12. Shine Ya ida aikin layin Jirgi na Kaduna zuwa Abuja.
 13. Lokacinsa aka ida gyaran Airport ta Enugu.
 14. Lokacinsa ne aka Gina Army University a Biu ta Jihar Borno.
 15. Lokacinsa ne aka Gina Jamiar Sufuri ta Daura.
 16. Lokacinsa ne aka Gina Makarantun Kimiyya da Fasaha na Kaltungo da Daura.
 17. Lokacinsa ne aka Gina manya manyan jami’o’i kusan 20 a Najeriya da manyan makarantun gaba da sakandiri masu tarin yawa.
 18. Lokacinsa ne aka sake Gina hanyar Zaria-Funtua-Gusau.
 19. Lokacinsa ne aka dauki matasa sama da Miliyan daya da rabi ake basu N30,000 duk wata har na tsawon shekara 2 a tsarin N-Power.
 20. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren bada bashin noma da ake cema Anchor Borrowers Program don inganta harkar noma a Arewa da Nigeria
 21. Lokacinsa aka fi daukar maaikata a kowane bangare na Gwamnati
 22. Lokacinsa ne ya Sanya hannun kan dokar cin gashin kai ta Kananan Hukumomi, yan majalissun jihohi da bangaren sharia na jihohi Amma gwamnoni suka ki aiwatarwa kuma jama’a su kayi shuru.
 23. Lokacinsa ne ya sake Gina hanyar Ibadan zuwa Lagos.
 24. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren bada bashin rance Loan Covid-19 da aka bawa miliyoyin ‘yan Najeriya makudan kudade.
 25. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren bada tallafi na SMEDan da aka bawa miliyoyin ‘yan Najeriya makudan kudade.
 26. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren bada tallafi TraderMoney da aka bawa miliyoyin ‘yan Najeriya.
 27. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren tallafawa matasa NYIF da aka tallafawa dubunnan matasa.
 28. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren tallafawa manoma a karkashin duk wata kungiyar Manoma na kowane irin abu da ake nomawa a fadin kasar.
 29. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren ciyar da daliban makarantur Firami na kasar baki daya.
 30. Lokacinsa ne aka fiddo da tsare-tsaren tallafawa ‘yan Najeriya a tsaruka da dama, wanda aka tallafawa miliyoyin ‘yan Najeriya.

Wa ‘yan nan kadan kenan daga cikin manyan ayyukan da za’a dinga tunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan ya sauka daga mulki.

Daga Yasir Mai-Taki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button