Videos
Martani hadi da umarnin sheike Ali pantami kan wakar Ado gwanja

Martanin Ali Ibrahim pantami kan sabuwar wakar fitaccen mawakin kuma jarumi masana’antar kannywood Ado gwanja
Ado gwanja dai ya sanar da sake sakin sabuwar wakar sa mai suna luwai inda ya alkawartawa masoyan sa tare da masu biyar sa
Ado gwanja dai tun bayan saki wakar sa mai suna chass a shekarar da ta gabata yayi kaura daga jihar Kano sakamakon ikirarin kama shi da hukumomi a jihar zasu yi
Mawakin dai na shan suka musamman a gurin malamai duba da yadda wakokin sa ke janyo wa mata haukacewa tare da shigo da wasu sababbin kalaman batsa
Malamai da dama dai na cigaba da nuna rashin jin dadin su kan wanna mawaki duk da cewa an haramta saka wakokin sa a jihar Kano musamman a gidajen Radio da talabijin