Masarautar Bauchi ta bawa Ali Artwork da Jamila nagudu sarautar Sardaunan samarin Arewa

Masarautar Bauchi ta bawa wasu jaruman masana’antar kannywood sarauta lamarin da ya sanya jaruman matukar farin ciki
Masarautar Bauchi ta karrama jarumai jamila nagudu tare da fitaccen jarumin barkonci Ali artwork sarautar Sardaunan samarin arewa
Wanna sarauta dai an basu ne a fadar Sarkin Bauchi inda mutane da dama ke cigaba da taya su fadin ciki kan wannan nadi da akayi musu
Duk da cewa wanna Bashir karon farko da aka bawa wani ko wata jaruma a masana’antar kannywood din sarauta ba amma wanna sarautar ta Ali artwork da kuma Jamila nagudu ta matukar dauki hankali
Yayin magantuwa kan wannan abun arziki da akayi musu Ali artwork ya bayyana matukar farin cikin sa bisa wanna sarauta da masarautar ta Bauchi ta basu inda suka sha alwashin taimakawa sarautar ta wane fuska
Jarumai a masana’antar kannywood da dama dai sun aikewa jaruman guda biyu murnar wanna sarauta da aka yi musu daga cikin su kuwa hards fitaccen jarumi kuma mai bada umarni Ali Nuhu