LABARAI/NEWS
Masha Allah A Kano An Daura Auren Marayu Biyu Mace da Namiji

Masha Allah A Kano An Daura Auren Marayu Biyu Mace da Namiji
Da amaryar da angon dukkanin su marayu ne wadan da suka tashi a gidan marayu na Nasarawa tun suna Yara
Yau an daura musu Aure Kuma anyi biki kamar yadda akeyin bikin Yayan dangi karkashin jagoranci kwamishiniyar mata Malama Zahra’u.
Amarya ta shiga da kafar dama domin kuwa a yau din wani bawan Allah Ganin yadda abu ya burge shi ya samarwa angon aikin yi domin rike amarya da kyau
Muna rokon Allah ya basu zaman lafiya ya albarkaci rayuwar auren su ya dawwamar da farin ciki a tsakanin su