LABARAI/NEWS

MASHHOOD ABIOLA (Shugaban kasar da bai yi Mulki ba… ABUBUWAN.11 DA YA KAMATA MU SANI AKAN MKO)

MASHHOOD ABIOLA (Shugaban kasar da bai yi Mulki ba… ABUBUWAN.11 DA YA KAMATA MU SANI AKAN MKO)

1 Ba ranar June12 ya mutu ba, ranar 7 ga July ya mutu ana saura kwana 17 ya cika shekara sittin a duniya

2 Ranar June12/ 1993 ne aka yi zaben da Abiola ke ikirarin lashewa.

3 Atiku Abubakar ba yau ya fara zaben fidda gwani ba, don ya kara da Abiola a kokarin cinye tikitin takarar Jamiyyar SDP wadda aka yi a Jo’s a watan Maris na shelarsr1993. Kenan Atiku na takarar kujerar shugaban kasa tun 1993 wato kusan shekara 30 kenan

4 Abiola ya biyo dan takarar Jam’iyyar Adawa har gida wato Marigayi Alh. BASHIR TOFA ya lallasa shi da ratar Kuri’a 14,810

5 Abiola ya shekara 15 a duniya kafin a rada masa suna Mash’hood saboda mahaifinsa Salawu ya haihu sau 22 duka suna mutuwa, Don haka ya gaji da yi wa yara suna suna mutuwa, Maimakon a yi bikin sunan Abiola a matsayin da na ashirin da uku sai aka sanya masa( Kashi mawo,) Wato kamar a ce Mu dan jira mu gani( Ko zai mutu) Sai da aka ga ya kai shekara 15 da ransa sannan a ka masa yanka aka sanya masa Mash’HUD, wannan ne ma’anar sunansa na M.K.O wato Mash’hud Kashimawo OLAWALE

6 Abiola dan Talakawan talau ne, Mahaifinsa na sayar da Koko,mahaifiyarsa Zulahaitu na sayar da goro,Shi kuma tun yana karami yake sayar da Icce ya taimaki iyayensa da kudin makaranta har ya koma rawan koroson yarbawa ana ba shi abinci don kada ya je makaranta da yunwa

7 Abubuwan da Abiola da Tinubu ke kama sune
-Kabila daya
-addini daya
-fitowa daga talakan gida,
-Duka Accounting suka karanta
-kwalakwalan idanuwa.
-gori (irinOluleh)
-sai uwa Uba Siyasar Its my turn da My Mandate

7 Yayi Ciyaman Na Jamiyar NPN ta su Shagari da fatan za a yi Mulkin Karba-Karba inda Shagari yayi shekara8 zai bashi takara, amma Manjo ya share wannan tsarin bayan da yayi wa Shagari Juyin Mulki

8 Abiola Member ne a kungiyar Musulamn Yarbawa ta Ansaruddin wanda shi ya wuce gaba a rigimar samar da Kotun daukaka kara ta Sharaar Musulunci a kudu maso yammacin kasar sannan ya bude makarantar Haddar Alqur’ani da sunan Mahaifiyar Zulaihatu Wuraola Sannan Yawan wucewa gaba a lamurran ginin Masallaci ya bashi damar zama abokin yan Arewa da kuma Rawanin Baba addini Of Yoruba Land

9 A wata rana cikin shekarar 1994 ne M.K.O ya sha fararen kaya ya kaddamar da kansa s matsayin sabon shugaban Lanjeriya Ya kuma kira sojoji da su hanzarta mika masa Emi Lokan dinsa, Maimakon amsa Bukatarsa Sai Shigaba Abacha ya tura motocin yansanda 200 suka zagaye mashiga da mafitar MKO har sai da suka damko shi

10 Shekara hudu MKO na sakaye a gidan maza, Kuma duk kokarin shiga tsakani da matsin lamba daga kasashen waje ya kasa samo masa ‘yancin fitowa daga gidan maza, Ko da yake a wani Yunkuri na shiga tsakani daga Kofi Anan, da Emeka Anyaoko shugaban kungiyar rainon Ingila ta Commonwealth, Sun samu Gwamnatin Soja ta amince da zata saki MKO amma da sharadin zai amince a sake zabe har ma ta kai Kofi anan da cewa, Majalisar Dinkin duniya ba zata iya ci gaba da mita akan zaben da aka yi ya wuce kusan shekara biyar ba, amma duk wani kokari na gamsar da MKO na ya mika wuya ya gagara ya ce shi fa Dole a bashi hakkinsa ko a ci gaba da rike shi

11 Abinda MKO ya sa a bakinsa na karshe shine ruwan shayi a wani zama da yayi suna tattaunawa da wasu turawa da ke kokarin shiga tsakani na ganin an saki shi, inda ya ce a bashi shayi ya wanke kwakwalwa, Amma tun bayan da ya kurbi shayin ne rayuwa ta rikice, ta inda duk wani kokarin likitoci na ceton ransa ya faskara har zuwa Mintuna90 inda ya ce ga garinku
ALLAH YA JADDADA MASA RAHMA

Wannan shine takaitaccen Tarihin Jagoran June12, A yi hakuri da karatu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button