ylliX - Online Advertising Network Masu cin gajiyar N-Power na Bauchi sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan a raba musu kudade - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Masu cin gajiyar N-Power na Bauchi sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan a raba musu kudade

Masu cin gajiyar N-Power na Bauchi sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari akan a raba musu kudade

Masu cin gajiyar shirin N-power a jihar Bauchi sun roki shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar da cika alkawarin da aka dade ana jira na yiwa masu aikin sa kai na N-power domin dogaro da kai da samar da ci gaba ga al’umma da kasa baki daya.

A watan Maris din wannan shekara ma’aikatar jin kai ta tarayya da hadin gwiwar babban bankin Najeriya (CBN) sun shirya taron horas da masu cin gajiyar sana’o’in hannu inda aka gabatar da shirye-shiryensu na kasuwanci.

Sanarwar mai dauke da sa hannun shugaba da sakataren N-power Ambassador da N-kiwon lafiya a Bauchi, Salihu Umar da Umar Yakubu Abubakar, kamar yadda ta kuma tunatar da cewa an kuma yi alkawarin za a fitar da kudaden a wannan lokacin, “Don haka muna hakuri da jira. ba tare da wata zanga-zanga ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button