LABARAI/NEWS

Masu garkuwa da mutane sun tattara iyalan wani mutu su 8 a garin ɗan-dume Katsina.

Masu garkuwa da mutane sun tattara iyalan wani mutu su 8 a garin ɗan-dume Katsina.

Bayan daukar dogon lokaci batare da masu garkuwa da mutane sun shigo garin Dandume ba.

Wayewar garin yau lahadi sun yi dirar mikiya a garin Dandume unguwar Dajin mare da misalin karfe 1:28pm inda suka shiga gidan sananne mutumin nan Alhaji Sani Na Buhari, bayan sun bincika basu ganshi ba suka tafi da iyalansa, matansa da yayansa akalla su 8 suka nausa cikin jeje tare dasu.

Yan Garkuwar sun dauki akalla kusan mintuna suna dukan kofar bata bude ba, wanda daga baya sukayi anfani da bindiga wajan fasa ginin kamar yanda kuka gani a jjikin photo suka shiga, bayan sun shiga kuma suka debi iyalan shi suka dinga jefusu ta cikin wannan hudar kamar wasu Awakai saboda kofar taki budewa.

Jami’ai sun iso bayan masu garkuwan sun shiga gidan wanda muna jin irin dauki ba dadin da’akayi dasu wajan hana yan ta’addan daukan iyalan amma hakan bai samu ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button