Masu ruwa da tsaki A jihar Bauchi karkashin mai girma Gwamnan Bala Muhammad sun ziyarci fadan Shugaban kasar Domin masa Godiya

Masu ruwa da tsaki A jihar Bauchi karkashin mai girma Gwamnan Bala Muhammad sun ziyarci fadan Shugaban kasar Domin masa Godiya
A yau ne Shugaban Kasar Nijeriya Muhammadu Buhari ya Karbi Tawagar Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, tare sarakunan jihar Wanda suka ziyarci fadar domin yin Godiya ga shugaban kasar.
Ziyaran na zuwa ne biyo bayan kaddamar da aikin samar da ruwan sha na garin Bauchi da shugaban kasa ya yi na naira biliyan 23.5 da hadin gwiwan Bankin Duniya (World Bank)
In Zaku tuna dai A ranar 19 ga watan Mayun 2022 ne sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya wakilci shugaban kasa Buhari zuwa jihar Bauchi yanda ya kaddamar da aikin a matatar ruwa ta Gubi da ke garin Bauchi.

Da yake jawabi ga tawagar da gwamnan ya jagoranta, shugaba Buhari ya gode masa bisa hada kan Al’umman sa na jihar Bauchi yanda suka fahimci zuwa suyi Godiya kan aikin alheri da aka yi musu hakan yana nuni da hadin kai da kaunar juna dake tsakanin ku inji shugaban kasar.

Sannan shugaban kasar ya yi alkawarin duba bukatun gwamnatin jihar Bauchi na kammala ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi a jihar da suke bukatar kulawar gaggawa domin kammala su.
Shugaban ya yabawa jihar Bauchi kan Yanda take da jiga-jigan ‘ya’ya ta suka taimake shi wajen cimma abubuwa masu yawa a Gwamnatin sa Sannan ya yaba da irin goyon bayan da alumman jihar Bauchi sukayi ta nuna masa tsawon tarihin siyasar sa.

Shugaban kasar ya bada misali da Ministan ilimin Nijeriya Adamu Mal Adamu Wanda Yace tsohon abokin sane da ya jima yana Tallafa masa cikin bagwarmaya rayuwar sa Wanda shima Dan jihar Bauchi ne,” inji shugaba Buhari.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed ya ce jihar ta ci moriya sosai a wannan gwamnati mai ci,na shugaba Buhari inda ya bayyana muhimman ayyuka a bangaren ilimi, ci gaban matasa, asusun horar da masana’antu, Noma, samar da ababen more rayuwa da kuma gina gidaje. Sannan ya kara ya ba wa shugaban kasa bisa kafa kwalejin ilimi ta tarayya, A garin jama’are, cibiyar fasahar kere-kere ta sojojin sama, A tafawa Balewa, kwalejin kimiyya da fasaha ta gwamnatin tarayya misau, jami’ar lafiya ta tarayya, kimiyar abinci da kimiyar likitanci, A garin Azare.

Tallafin firamare. ilimi ta hanyar hukumar ilimi ta duniya (UBEC ). Gwamnan ya bayyana cewa ta hanyar tallafin gwamnatin tarayya jihar Bauchi ta samu naira biliyan 12 domin gina gidaje 2,500 a fadin masarautun jihar. “Wannan shi ne karo na farko da muke da tsarin gina Gidajen a fadin Masarautu jihar ta Bauchi.
kuma na san iyayenmu masu sarauta dake tare dani a yanzu su shedu ne kan wannan Ayyukan. Kuma za suyi godiya ga gwamnatin tarayya kan wannan karimcin,” inji Gwamnan
Gwamnan ya Kuma shaida wa shugaban kasar cewa duk da irin bambance-bambancen jam’iyyar siyasa a halin yanzu Shugaban ya cigaba da nuna kauna ga Al’umman jihar Bauchi saboda kishin kasa da kuma dagewa wajen ba da fifiko wajen bunkasa ababen more rayuwa a kasar nan. Ba tare da nuna Bambamci ba.
‘’Akan hakar Mai, ya zamo wajibi mu gode muku da kuka ba da fifikon ayyukan hakar man a Arewa musamman aikin mai na Rijiya Benue da kuma namu na jihar Bauchi da Gombe .
Muna gode muku da kuka ziyarci wurin binciken da kuma nuna kishin ku na ci gaban Arewa a wannan fannin Dan Inganta tattalin arzikin kasar nan ,’’ inji shi.
Gwamnan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gina hanyar Daga Alkaleri zuwa Gombe-Abba saboda hakar man fetur da ake yi a yankin. Sai kuma aikin hanyar Jos-Bauchi -zuwa Gombe .Wannan aiki ne mai matikar muhimmaci a Yankin Arewa da muke fatan ganin ya tabbata Muna da Yakinin za’a tabbatar da wannan fata namu.










Lawal Muazu Bauchi mai taimakawa gwamnan Bauchi kan Sabbin Kafafen Yada Labarai na zamani.
Mayu 25, 2022