LABARAI/NEWS
Masu satar mai ne su ka haddasa fashewar tankar mai a Hukumar kwana kwana

Masu satar mai ne su ka haddasa fashewar tankar mai a Hukumar kwana kwana
Hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ta ce satar mai wasu ɓatagari su ka yi daga wata tankar man fetur da ta fadi su ne suka haddasa gobarar da ta tashi
Nan da nan mu ka dauki adireshin wurin mu ka kuma tura jami’an kashe gobara karkashin wajen wutar ba tare da bata lokaci ba aka kashe wutar
Da isowar jami’an rundunar kashe gobarar su ka fara aiki tare da kashe wutar gaba daya
A cewar masu binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa gobarar ta afku ne sakamakon wata tankar man fetur da ke dauke da na wacce kai ya kwace ta fadi a gefen titi