LABARAI/NEWS

Mata 255 sun shiga aikin jami’an tsaro na aikin Hajji a Saudiya

Mata 255 sun shiga aikin jami’an tsaro na aikin Hajji a Saudiya

 

Karkashin jagorancin ministan harkokin cikin gida na kasar Saudiyya Yarima Abdulaziz bin Saud bin Naif Daraktan Tsaron Jama’a Laftanar Janar Muhammad Al-Bassami a ranar Laraba ya halarci bikin yaye mata 255 na jami’an tsaro na musamman

 

Sun kasance kashi na hudu na mata da aka dauka aiki wadanda su ka kammala karatu a Makarantar horas da Sojoji ta da kwararru kan harkokin tsaro na Hajji da Umrah

 

Za su shiga cikin runduna ta musamman mai kula da harkokin diflomasiyya da jami’an tsaron Hajji da Umrah

 

Matan da su ka kammala karatun da ɗaukar horo sun sami horo kan aikace-aikacen da fasahar sadarwa, da kuma darussan akida da na aiki kan dabarun da ake bukata don gudanar da ayyukan tsaro

 

Haka kuma sun samu horo kan tsari da tsarin aikin tsaro, baya ga shirya su kan wasu ayyuka na musamman da ake bukata domin gudanar da su daidai da yanayin aikinsu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button