LABARAI/NEWS

Matar shugaban SSS ta umarci jami’ai su kama Abba Kabir, kuma su hallaka guda cikin hadimansa

Matar shugaban SSS ta umarci jami’ai su kama Abba Kabir, kuma su hallaka guda cikin hadimansa

 

Aisha Bichi wacce mata ce ga shugaban hukumar tsaron farin kaya SSS Yusuf Bichi tayi umarnin a kama dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf (Abba Gida Gida) domin hana shi hawa jirgin Max Air daga Kano zuwa Abuja

 

 

a daren ranar Lahadi sakamakon tsaiko da tawagar Abba ta janyo a filin sauka da jiragen sama na Malam Aminu Kano dake Kano

 

Aisha lamarin da yasa jami’anta suka fara dukan mutane da ababen hawa bisa rashin girmama Madam har sai da shi Abba ya shiga dakin jira ya same ta tare da korafi bisa abinda jami’an tsaro suka aikata ga mutanensa

Wata majiya ta bayyana cewa yayin da Abba ke mata bayani sai ta fara fadar maganganu marasa dadi akansa dukda wani babban jami’i na bata hakuri amma ta cigaba har tana mai cewa ba zata bari Abba ya zama gwamnan jihar Kano ba, kamar yadda majiyar ta bayyana

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button