ylliX - Online Advertising Network Matasa sun yi wa wata bazawara tumɓur a Enugu bisa zargin ɗiban dodon-koɗi a wani keɓaɓɓen jeji - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Matasa sun yi wa wata bazawara tumɓur a Enugu bisa zargin ɗiban dodon-koɗi a wani keɓaɓɓen jeji

Matasa sun yi wa wata bazawara tumɓur a Enugu bisa zargin ɗiban dodon-koɗi a wani keɓaɓɓen jeji

Anthonia Okonkwo, matar da ake zargin wasu matasa ne sun yi wa tsirara a jihar Enugu, ta ce ba ta ɗebi dodon-koɗi a keɓaɓɓen jejin da a ke bauta ba kamar yadda waɗanda su ka dake ta ɗin su ka yi zargi.

Okonkwo ta bayyana hakan ne a yau Juma’a a lokacin da wata kungiya kare hakkin mata mai zaman kanta, WACOL, karkashin jagorancin Farfesa Joy Ezeilo, ta kai mata ziyara a wani asibiti da ke Afam-Mmaku a Ƙaramar Hukumar Awgu ta jihar.

Da take ba da labarin abin da ya faru da ita, matar mai shekaru 44 da haihuwa ta ta ce ta dade tana girbi tare da sayar da dodon-koɗi domin ciyar da ƴaƴanta hudu tun bayan mutuwar mijinta shekaru 13 da suka gabata.

Ta ce, a ranar da abin ya faru, ta na gidanta sai ta ji hayaniya a waje, sai ga matasa sun mamaye gidanta, suka fito da ita, ba tare da samun damar kare kanta ba.

A cewarta, sai matasan su ka fara dukanta da makamai da kulake, inda suka tube mata tsirara tare da daure mata sabbin dabino a kugu da kuma wuyanta wanda ke nuni da wani aiki na tsafi a cikin al’umma.

Ta ƙara da cewa ta ji takaicin yadda ɗan uwanta da ya zo ceton ts shi ma sai da aka haɗa da shi a ka yi masa dukan tsiya sabo da ita.

Okonkwo ta lissafa sunayen wadanda suka aikata mata ɗanyen aikin da suka hada da Sunday Nwangene, Jonathan Nwangene, Obi Nwangene, Chigazu Okpala, da Okechukwu Okeke.

Sauran sun hada da Chukwudike Anikene, Chukwuebuka Agu, daya Maduabuchi da mahaifinsa da kuma wata yarinya da ta dauki hoton bidiyonta yayin harin.

Kawo yanzu dai rundunar ƴan sandan ta cafke mutane bakwai da ake zargi da aikata laifin, yayin da wasu kuma su ka tsere.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button