ylliX - Online Advertising Network Matashin Da Aka Sace Wa Babura Masu Kafa Uku Ya Kashe Kansa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Matashin Da Aka Sace Wa Babura Masu Kafa Uku Ya Kashe Kansa

Matashin Da Aka Sace Wa Babura Masu Kafa Uku Ya Kashe Kansa

Wani matashi mai shekaru 25 a Jos, babban birnin Jihar Filato, ya kashe kansa sakamakon sace masa Keke Napep guda biyu mallakin ubangidansa da wasu batagari suka yi.

Rundunar ’yan sandan jihar ta ce bayan tsintso gawar matashin a dakinsa, tana zargin ya rataye kansa ne a ranar da wani ya ritsa shi da bindiga ya kwace masa babur na biyu.

Wani dan uwansa na jini mai suna Mista Adukuchili Angai ya bayyana wa Aminiya cewa matashin ya dauki ransa ne sakamakon damuwar da ya shiga.

A farkon shekarar nan ne marigayin ya samu hayar babur mai uku a hannun wata mata don ya rika aika mata kudi kowanne mako, abin bakin ciki, sai ya ara wa abokinsa amma aka sace.

Matar ta kai shi kara gurin ’yan sanda aka kama shi, sai da ya yi sama da mako guda a hannunsu, sannan aka sake shi tare da neman ya biya kudin babur din da kadan-kadan.

Ya fara biya makonni kadan sai kuma ya kasa ci gaba, sai ya tunkari wani mutum mai babur din da zummar yin aiki ya aika masa kudin a kullum, don ya samu biyan wancan babur din da aka sace.

Sai dai a ranar 13 ga watan Oktoba lokacin da yake dawowa gida daga aiki sai wani mutum dauke da makami ya kwace babur din Ya dawo gida cikin bacin rai ya hadu da wasu abokansa inda ya bayyana musu abin da ya faru kuma ya yi barazanar kashe kansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button