Fadakarwa

Mazaje kuji tsoron Allah

Auzu BILLAHI minasshaitanir rajeem, BismiLLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM.

Assalamu alaikum warahmatuLLAHI WA barakatuh.

Walhi ba hassada bah, kuma ba qiyayya bah face don soyayya da kuma addini kada ya samu matsala, a shiga rudani, a rasa inda bakin zare yakke alhalin mu muka faroshi.
Mafi tsoritarwa a wanga sabuwar fitowan mah shine, zakaga ba wai mata baneh sukke promoting din abin acikin mata, agidaje don a amfana, a’a wato masifar shine mazaje ne ke ma ruruta abin a waje wa mazaje. Wai tayi gadon masallacin da babanta shima ya karantar. Wa iyazubILLAHI. Da annabi ya rasu, dake shi ma wa’azi ya dinga yiwa sahabbansa, Nana Fatima batayi gadon masallaci bah da sunan itama, tana karantarwa. Wannan irin tunanin yana daga cikin abinda ya haifar da shee’ah, fitina babba da ta mamaye musulmin duniya.

Kasancewa a yanzu duniya ta tsuffa, tazo qarshe, abubuwa da yawa Wanda ba addini bah zasu na bullowa da sunan addini. Kuma wannan maganar wa’azin mace a masallaci yana daga cikin masifun qarshen zamani. Banqi bah a biranenda babu musulunci sossai sai yanzu musuluncin ke tasowa. Amma banda kamar Nigeria, masifa kawai zai haifar. Inda ba a sha ilimin addini sossai bah, za’a bassu uzuri Wanda tabbas suma nan gaba kadan, idan ilimin addini ya yadu, zassu fahinta su daina. Yawancin su basuda girman kai, idan gaskiya yazo musu. Amma yan duniyar Nigeria sai a hankula, girman kan tsiya, sai mutum ya noqe ga gaskiya qarara a gaba gareshi.

Manzon ALLAH yabamu labari yana cewa sahabbai au kama qaala Idan suka yi nisan kwana za su ga sababbin abubuwa amma ga shawara, su bi sunnarsa da sunnar khulafa’ur -rasheedeyn, suyi riqo da sunnar da fiqoqinsu… Maganar suyi riqo da fiqa ’emphasis’ ne, sabida manzon ALLAH yasan wahala gareshi a qarshen zamaniy. A wani hadithin yace sabida a nuna maka yadda riqo da sunnar manzon ALLAH S.A.W da kuma khulafaa’ur rashideeyn da qarni ukun farko, manzo SAW yace masu riqo da sunnata kamar mutum ne ya damkqi garwashin wuta sabida tsananin zagi da aibanta da jahiltarwar bogi da za’ayi musu da kuma nunawa da za’ayi a idon duniya cewa Kansu bai waye bah da sauransu. SubhanALLAH!

Mace a masallaci tana karantarwa kuma wai tafseeri?

Bamu ce wane, malaminda kuka yarda dashi bashida ilimi bah amma kuma ba annabi baneh shi kuma kun sani, kuma bai kai ko darajan takalmin sahabi bah, da zakuce maganarsa itace ‘kankad.’ Yawancinsu sai suceh maka ai tuni Dr wane ya yi mana bayani. Kawai da yawa ka rasa meke damunsu. Wassu fah idan aka ce musu Doctor wane ne, toh suna masa daukar ya wuce kuskure, ko Professor wane sunayi masa kallon yafi sahabi, sai kaji ance musu sayyidina Abubakar, Umar, Uthman, Aliy, da manya-manyan sahabbai ko dikkan mitanen madina basuyi bah ko akan tafarki kaza sukke, ridwanuLLAHI Alaihim, sai kaji an yanko maka tsakiyar wani hadithiy, ba farko, ba karshe.. A yi ta yin kame-kame. Shiyassa malam ya kirasu da yan tsalle-tsalle. Da yawa bah addini baneh a gabansu, neman suna da shahara.

Ko a cikin wannan rudanin idan kaji yadda sukke wasa yar-sheikh Ja’afar, kai kace ilimin addinin duniya akanta yakke. Kamar babu mai wata fatawa ingattatta in ba ita bah. Kanaji kasan wannan shuhra kawai ke gabansu.

Sa’annan da ace suna tambayar malumansu, ba su kasancewa kamar gawa a gaban mai wanketa, misalin cewa;

Ummil Mu’mineena Nana Aisha R.A batayi hakanan bah, ita dake uwar muminai mah guda, Wanda aure ya haramta ga wani rayayye a gareta, dikda hakka batayi irin wannan karantarwar bah. Ta shiga masallaci tana karantarwa? Irin wannan na qarshen zamanin?? Ko kuma wani mole zaice mana babu masallaci a wancan lokacin, ko ba’a buqatar ilimi a wancan lokaci??

Ko wani abu a musulunci idan ya halatta toh akwai yadda akeyinsa, idan yadda akeyinsa ya saba da sunnah to yazamto bidi’a.

Sannan sauran matan Annabi Muhammad SAW bamu da labarin sun tsunduma masallaci suna karantarwa. Su tambayi malumanda suka yarda dasu in akwai.

Ni dalibi ne na baya-baya amma ina son maslahan al’umma bisa abinda ya tabbata a Sunnah.

Ku fahimta dalla-dalla don ALLAH ya ku yan’uwa, maudu’in da ake magana shine karantarwa a cikin masallaci, ba karantarwa kawai bah. Kada Ku gudu daga filin dagan, Ku koma yin musu akan abinda ba shine akke magana akai bah. Ni ba nazo musu baneh, inaso in fahimtar ne iya gwargwado amma idan aka zageni wannan daman ba abun mamaki baneh.

Malaman zamani zasuyi kotolo, suyita kalen dalilan hakan, amma basuda magabaci a qarni guda uku na farkonda annabi SAW yace sunfi kowanne alkhairi kuma muyi koyi dasu.
Su qarnin farko basuyi hakah bah. Munfisu gane addinin ne ko yaya. SUBHANALLAH.

Abunda ya tabbata daga sunnah; Idan mace tana da karatu, shine ta tusa yaranta a gabanta ta yi musu karatu iya karatu. Ko kuma a makarantar islamiyya ko higher Islam tazamto malama mai karantar da littatafai, Su kuma su futa wajen duniya su karantadda al’umma. Idan kuma daliban mata ne su, su ma su karantarda yaransu, sabida su taso da tarbiya ingattatta. Hakanan bi da biy sai dikka al’ummah ta gyaru, amma ba wai tashiga masallaci bah, ita bah muharramah bah, tana karantarwa koh bah lasfika, matukar masallaci neh, wanda maza ke zuwa sallolin khamsus-salawaat, bai halatta bah. Babushi a musulunci.

Annabin mu, Muhammad SAW da Umar R.A sun kasance suna discouraging mata zuwa masallaci sallah, wato suna qarfafa musu yin sallah a gidajensu yaffi akan suje masallacin annabin da kansa, wannan kuma baya nuni cewa a hanasu. Kada Ku hanasu zuwa masallaci amma Ku nuna musu yinsu a gida shi yafi alkhairi inji ma’aiki SAW. Akwai kuma hadeethai akan wannan. Wato misali kai ne, kacewa matarka kada kije masallaci, kamar yadda sayyidina Umar yayi, sai taqi, toh bah halin ka hanata. Sabida maganar annabi SallALLAHU Alaihi Wasallam akan kada a hanasu, sabida akwai yanayinda zai sa dole taje, misali a makaranta, ko taje office yin aiki, ko taje banki, lokacin sallah yayi ko wani waje wanda addini bai hana zuwa bah, kaga babu makawa, wannan zataje masallaci sabida ba’a karhanta bah. Amma tana gida, a futo da ita, annabi bai qarfafa hakan bah, kamar yadda ya tabbata a hadeethi. SubhanALLAH! Amma wai yau wanine ko wata ne zata na qarfafa futdo da mata daga gidajensu zuwa masallaci sallah ko kuma ma har wa’azi a MASALLACI?

SubhaNAALLAAH! subhaNALLAH!!.

Matan Annabin tsira sallAALLAHU alaihi wa sallam basuyi bah, na sahabbai basuyi bah, tabi’ai basuyi bah. Kuma Wannan a addini, hakkah addini ya tsara. Hakan a addini, yana nesanta tsakanin taron maza da mata da kuma nesanta yawan fitar mata barkate inda zasu zamo arha ga mazaje, fitsara ta samo gindin zama. Abinda yasa kuwa sabida ALLAH ya sanya soyayyar mace a zuciyar maza, haka ma mata. Kuma mutum bai isa ya tambayi ALLAH miyasa bah. Toh sai shi ALLAH din ya ajiye mana dokoki. Yawan futan mata, ko yawan kusantansu ga maza toh zai karkatar da zuciyoyin mazaje zuwa abubuwanda basu da wani muhimmanci. Akwai hadithin da ke maganar karkatarwar da mace takkeyi har ga mu’minai masu bin ALLAH sawu da qafa.

Dokar ALLAH, akwai hana mata yawan futa, har ko da masallaci ne. Annabi ya qarfafa cewa kada suje.

Shaitan kuma baya yin barna lokaci guda, a hankali yakkeyi, zai sa ka yin wani abunda kake tunanin hakan dai-dai ne, sai idan ALLAH Ya tsamar da kai ka lurra sossai tukunna. Idan baka lurra bah, ALLAH Ya turo da wani dalili cewa ka ankara. Idan kaqi ankara, ko ka ankara latti kamar yadda fir’auna yayi, toh babu abin zargi face, kanka.

Idan muka hango hadithai da dama zamu gane hakanan cewa kullun mace a gida yafiye mata alkhairi.
Ayar alqur’ani, fadin ALLAH madaukain sarki kuma ya rigaya ya tabbatar da wannan.
وقرن في بيوتكن ولا تبرجن تبرج الجاهلية الأولى ۖ وأقمن الصلاة وآتين الزكاة وأطعن الله ورسوله ۚ إنما يريد الله ليذهب عنكم الرجس أهل البيت ويطهركم تطهيرا
[Ahzaab : 33 ]. ” Su zauna a gidaddajensu, kada suna tabarruji, yawan fita da nuna Kansu kamar yadda Jahilan farko sukeyi….” Inji ALLAH ubangijinmu.

Wani Misali kuma idan ka lurra da sahun sallah na mata da maza tunda ba haramun baneh acikin hadithiy

فقد روى مسلم في صحيحه عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ خَيْرُ صُفُوفِ الرِّجَالِ أَوَّلُهَا وَشَرُّهَا آخِرُهَا وَخَيْرُ صُفُوفِ النِّسَاءِ آخِرُهَا وَشَرُّهَا أَوَّلُهَا.هـ. والحديث رواه ـ أيضا ـ أحمد وأهل السنن الأربعة فهو حديث ثابت صحيح.

Mafi alkhairin Sahun maza shine sahun farko, mafi sharrinsu shine na qarshe, mafi alkhairin sahun mata kuma shine na qarshe, mafi sharrin sahun mata shine na farko.

Abin lurra anan shine sahun da yafi kusada ‘opposite sex’ shi yaffi sharri sabida yafi kusada jinsin da ba nasa bah.

Hakan yasaka sayyidina umar aka ruwaito cewa yana cewa: Ku nesanta tsakanin nunfashin maza da numfashin mata.

فروى ابن القاص الطبري في أدب القاضي (١١٦) بسنده عن عمر رضي الله عنه قال: ( باعدوا بين أنفاس الرجال والنساء ).
والمقصود من الأثر النهي عن مخالطة الرجال النساء الأجانب والعكس فإنَّ ذلك يسهِّل الوقوع في الفتنة والمحرَّمات، والعياذ بالله.
والله تعالى أعلم.

Wa’azin mace a Masallaci ko kadan bashida asali a addini.

Za’a iya baiwa mace muqami a addini (ba kowanne bah), ko kuma taje filin yaqi, dikka akwai a musulunci, amma wa’azin mace a masallaci bamusanshi bah daga matan Annabi SAW, kuma bamu samo bah a sahabbansa. Kuma dalilai sun gabata iya gwargwado. Masu kotolo zasu yi kotolonsu amma mata anfison su karantar a gidajensu, sabida ko Nana Aisha ma da take uwar kowa a muminai, haramun wani ya nemeta da aure, a haka bata zo masallaci tana karantarwa bah, dik tarin iliminta a gida ta bayar. Annabi yace Ku riqi Rabin ilimin addininku a gurin wannar yar ja din. Dikda hakka bata shiga masallaci tana karantarwa ana zaune a gabanta bah.

Sheikh Ismaila idris, ALLAH YA mai gafara, amin, mahaifiyarshi ta koya masa alqur’ani, shi kuma ALLAH YA qaddara har ya kafa kunqiyar izala, wannan shine asalin sunnah.

ALLAH shine maffi sani, ni ba kowa baneh kuma bah komi baneh. Amma inason maslahan al’umma kuma zan fadi gaskiya ko da akan kaina ne. Bissalam wa BILLAHIT-TAUFEEQ.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button