FadakarwaIslamic Chemist

ME YA KAMATA AYI IRIN WANNAN LOKACIN NA ZAFI

ME YA KAMATA AYI IRIN WANNAN LOKACIN NA ZAFI

A irin wannan yanayi na zafi wajibi ne mutane su yawaita shan ruwa koda basajin kishi domin kare lafiyar sassan sarafa abinci tare da tace jini ajika wato uwar hanji (stomach) da koda (kidney).

Sannan aguji kwanciyar cunkoso kada sama da mutum 3 suke kwana cikin daki guda, koda kuwa yara ne a anzuba da yawa su 4, Sannan a tabbatar da anbar kofa abude🏠 tare da tagogi domin asamu shige da give din iska yake ratsawa (ventilation).

Gidajen kallon kwallo (viewing centers) ko Cinemas, Gidan Party da sauransu nan ma anisanci zama acushe, Sannan wajibine kasan waye kusa da kai saboda kare kai daga cuttukan dakan bi iska su yadu da akan iya dauka ta numfashi, tari, ko zufa ciki kuwa harda ciwon hanta.

Ba laifi bane ka sami karamin mafeci ko kwali ka rike aduk lokacin da mutum zaije irin wadannan wurare saboda ya rika fifita akai akai.

Sannan a kiyaye zama acikin rana na dogon lokaci tabbas akwai hatsarin kamuwa da rukunin ciwon cancer na fata musamman wanda mukan Kira da Basal cell carcinoma.

KASHI NA BIYU

Sannan wannan lokaci ne da cuttuka irin su hangun (mumps), kyanda wato (measles) ko ince bakon dauro a hausance da Varicella wato ƙarambau ke cin kasuwarsu.

Duk da sau ɗaya ake iya yin ciwon kyanda a rayuwa amma yana da hatsari, wato de in anyi sau daya ba a kuma maimaitawa Saboda Kwayar virus din ko ankuma haduwa da ita bazatai tasiri ajika ba saboda garkuwar jikin da jiki ya samar na gubar (humoral immunity).

Tohfa saide musani wannan ciwo na kyanda yana da matukar hatsari yakan yadu cikin kankanin lokaci Sannan yakan iya haddasa makanta (blindness), kurumta (deaf), kuraje, ciwon baki da kuma lalata sashim cikakken saiti na kwakwalwa yadda zakaga mutum ba mahaukaci bane tabbas! toh Amma kwaisa da rashin kangado, ko kuma wani susu. Sannan tana jawo saurin mantuwa, ciwon zuciya, koda, kai harma da kashe kwakwalwa tare da shi wanda ta kama din babba ko Yaro.

Don haka adage dakai yara rigakafi. infact koda baki rika kai yaron ki rigakafi ba matukar ya kai wata tara akaishi ya kar6i rigakafin kyanda. Idan har ta tabbata ana fama da annobarta to Yaro har dan wata 6 zaai masa basai yakai wata 9 ba. Sannan da anga mai ciwon ai hanzarin ke6esa agida (isolation) ai hanzarin kaisa asibiti.

Sannan yayin kwantar da yara masu kyanda kar a kuskura ake kwantar dasu ta rigingine ko ruf da ciki “wato ya zamto fuskarsu na kallon sama ko keyarsu na kallon sama wannan kuskurene dake ba Kwayar cutar damar ta6a kwakwalwa nan take koma yaro ya mutu.
Don haka a tabbatar ana kwantar dashi a hannun dama ko hagu shine daidai.

KASHI NA UKU

A duk lokacin da zamui tari ko atishawa a irin wannan lokaci muke sa wani abun muna tarewa musamman handkchief Saboda gujewa yada cuttuka. Inma baka da handkchief ka jawo coller din rigarka ko hannun ki Rigar ka/ki yi ajiki.

Inma kuma Rigar mai gajeren hannu ce in tare kuke da wani yi amfani da bayansa kai atishawar ko tarin abayan Rigar wanda kuke tare hakan shi yafi dacewa fiye da ka saki abun a iska zaka iya cutar da mutane masu tarin yawa.

KASHI NA HUDU

Shawarata ta karshe adage da wanka sau 2 zuwa 3 arana, musamman yayin kwanciya bacci da daddare akama yara a wanke su fess suma.

Sannan musamman yara mata kanana iyaye yayin musu wanka bakwa sa hannu ku cude musu gabansu sosai saide ku barsu sui da Kansu!

Wannan kuskurene ana samun distortions na bacteria shikesa wani yaron da zaku kai musu ziyara sanna suke baci zakuga hannunsu a wando ko siket suna susa Saboda kaikayi na zufa tunda ba wajene da iska ke ratsawa ba wannan ma haka yake a yaren da ba’ai ma kaciya ba maza da yawa zaka sami hannunsu a wando,
wani sai anta fama dashi ma bakomi ke jawo irin haka illa tun suna kanana kwayoyin cuta sun rika shiga kafar azzakarinsu batare da ana tudota a wanke musu ba, don lokaci lokaci ake tudo fatar ana wanke musu da ruwan dumi, haka ma yaya mata kanana da kanku zakuji yaukin na fita inkuna wankesu.

Allah yasa mun fadaka Amin.

[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button