LABARAI/NEWS

ME YASA AKA DAUKE BIRNIN TARAYYAR NIGERIA DAGA LAGOS ZUWA ABUJA

ME YASA AKA DAUKE BIRNIN TARAYYAR NIGERIA DAGA LAGOS ZUWA ABUJA

Jiya nace; a cikin ajandar mutanen can masu fifita kabilanci akan addini da dukkan rayuwarsa, suna da ajandar mayar da birnin Tarayyar Nigeria Lagos daga Abuja

Sai na fahimci akwai wadanda da basu san cewa a farkon tabbatuwar Nigeria birnin tarayya yana Lagos bane kafin a dawo dashi Abuja

To abin tambaya anan kun san dalilin da yasa aka dawo da birnin tarayya Abuja daga Lagos?
Kuma kun san dalilin da yasa suke da ajandar sake mayar da birnin tarayya Lagos?

Akwai dalilai masu dumbin yawa da yasa aka dawo da birnin tarayya Abuja, babba daga cikin dalilan shine KABILANCI da ake nunawa wadanda ba yarbawa ba a Lagos

Tsohon shugaban Nigeria a mulkin Soji marigayi Janar Murtala Muhammad shine wanda ya fara yunkurin dawo da birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja a shekarar 1976, har zanga-zanga sai da sukayi domin su dakileshi a wancan lokaci

Ya gabatar da wannan kudurin kenan ba da jimawa ba suka masa kisan gilla ta hanyar harin kwanton bauna a ranar 13-1-1976 yana tafiya ofishinsa dake Dodan Barracks Lagos

Tun daga lokacin sai manyan mu na Arewa suka ji tsoron dauke birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja saboda rashin adalcin da ake yiwa ‘yan Arewa da sauran kabilun da ba na wadancan mutane masu Kabilanci ba

Sai a shekarar 1991 aka samu wani gwarzon shugaban Nigeria na mulkin soja ma’abocin kishin Arewa da addini General Ibrahim Badamasi Babangida ya samu nasaran dauke birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja

Abuja itace tsakiyar Nigeria Kasar da kabilunta tsiraru ne, an yiwa kowani yanki na Kasar adalci kenan, don Allah na bawa karnukan farautar Tinubu assignment ku je ku binciki dalilan da abubuwan da suka faru wanda yasa shugabannin mu na Arewa sukayi tsayuwar daka suka dauke birnin tarayya daga Lagos zuwa Abuja

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button