Islamic Chemist

ME YASA MUTUNE SUKE YAWAN TUSA??

ME YASA MUTUNE SUKE YAWAN TUSA??

ME YASA MUTUNE SUKE YAWAN TUSA??

Ga kadan daga cikin dalilai wadanda ke haifar da yawan TUSA.

– Haduwar ko samuwar yawan bacteria a cikin tinbi

– Yawan anfani da fibrous foods

– Yawaita anfani duk wasu kayan abinci masu dauke da sanadarin malt extracts

– Matsalolin ciki ko cutukan da suka shafi GI tract kamar gastroenteritis

– Irregular bowel movements ko Kuma bushewar ciki

– Abinci ko ruwan da basuda cikakkar tsafta na daga cikin dalilan dake haifar da yawan TUSA

– Yawan anfani da high-fat diet wadanda ke Samar da yawan carbon dioxide, daga karshe mutane suyi ta fitar da iska.

– Wasu masu yawan TUSA tana faruwa sanadiyar metabolic breakdown na sanadarin sulfur-containing proteins da kuma amino acids a intestines kamar Wake

Amma Kuma yawaita yin Tusa ko tsanantar Tusa na tabbatar da wata matsala a jikin Dan Adam wacce take bukatan bincike Mai zurfi

A WANI BANGARE KUMA YA KAMATA MUTANE SU SAN WADANNAN ABABE 12 AKAN TUSA

– A yaren Hausa, TUSA ko HUTU, na nufin fitar da iska daga dubura.

Duk da kasancewar kowa na yin TUSA, Hausawa na ganin yin ta a gaban mutane abin kunya ne.

Da yawan mutane basu san menene ke saka fitar TUSA ba ko kuma wane amfani fitar ta ke yiwa jiki ba. Hakan ne ya saka muka kawo maku wasu muhimman abubuwa guda 12 a kan TUSA kamar yadda binciken masana ya tabbatar.

1. Maza sun fi Mata yawan yin TUSA.

2. An fara bincike a kan TUSA tun shekarar 1962.

3. Mutum mai lafiya kan yi tusa a ƙalla sau goma sha biyu (12) a rana!

4. Adadin iskar TUSA da mutum ɗaya kan fitar a rana za ta iya cika robar balan-balan da iska.

5. Fitar TUSA alama ce ta kyawun aikin hanyar sarrafa abinci a ciki. Ga duk wanda baya samun yawaitar yin TUSA, ya garzaya domin ganin likita.

6. Shaƙar iskar TUSA yana da matukar mahimmanci saboda sinadarin HYDROGEN SULFIDE da ke cikinta.

7. Tusar Mata tafi ta maza wari saboda yawan sinadarin Hydrogen Sulfide da tusar su ta ƙunsa fiye da ta Maza.

8. Tusar ku (ya ku ƴanuwa)

Tana tafiyar ƙafa goma cikin daƙiƙa guda (10ft/sec.).

9. Tusar masu karamar kofar dubura ta fi kara saboda iskar ba ta samun wadatacciyar ƙofar fita.

10. Yawan taunar cingam (Chewing Gum) da shan lemukan kwalba masu ‘gas’ na saka mutum yawan TUSA.

11. An fi yin TUSA yayin barci!

12. Kiyashi ya fi kowacce dabba yawan yin TUSA duk da Ƙanƙantar sa. Dangin Raƙuma ke biye da kiyasai wajen yin TUSA, sannan sai Jakin dawa (Zebra) da dangin Shanu.

Mutum kan ji daɗi bayan fitar tusar. Yin tusa samun lafiya ne, ku saki abar ku duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Saki tusar ka ko gaban sirikin Kane Alhaji iyaka yace yaro Allah ma Albarka 😅😅😅😅 Yusura Yasir Kangiwa , Bilkisu Lawal Saidu , Nauwara Almustapha , Mas’ud Ahmed Yari , Ummu Khalid , Zaliha Yahaya Bello , Saratu Ibrahim Bebeji

Allah Ya bada ikon yin TUSA, amin.

Ayi TUSA lafiya!!! 😊

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button