ME YASA NAKE WA YAN SHI’A ADALCI?

ME YASA NAKE WA YAN SHI’A ADALCI?
Daga: Aliyu Samba
Waɗansu Shekaru baya na kasance daga cikin waɗanda suke nuna ƙiyayya ta tsana ga mabiya mazhabar Shia. Na taso a gidan Sufanci tsakanin mabiya ɗariƙar Muridiyya da Tijjaniyya, around 2006 na soma shiga cikin mabiya karantarwar Salafiyya. Salafanci ya shiga raina a wannan shekarun saboda kwaɗayin iya yaren larabci, har ya kusan bin jikina.
A tsakanin Shekaru 3 na samu zuwa tarukan IVC (Islamic Vocational Course) da Kungiyar MSSN ke gabatarwa duk shekara, a wannan lokacin na tasirantu matuƙa da karantarwar Salafiyya, musamman da Allah yasa na taso a tsarin sufanci, sai na zaci dukkan malaman addini masu kafewa ne kan gaskiya saboda suna da wata baiwa ta iya Fassarawa da yada saƙon Allah.
An sanar dani miyagun akidun Shi’a, da yadda suka barranta daga Musulunci, an koyar dani cewa ibada ce ma kyamatarsu, kyararsu da tsanar su, nakan iya tuna wani malami mutumin Guru a taron IVC na karshe da naje yake cewa damu ya halatta ma kayi karya don cetan mutum daga afkawa Shia, wannan gaɓar itace ta soma samun shakku.
Dawowa ta daga wannan taron na baiwa kaina ƴancin nasan mecece aƙidar Shi’a daga wadanda suke Shi’a, cikin ikon Allah sai na gamu da littafin nan “When I was guided” na wani malami wanda a baya Sufi ne, daga bisani ya zama dan Shia. Wannan Malam mai suna Muhammad Attijaniy Assamawiy yayi bayani cikin wannan littafin nasa da ma wasu daban da suka sanya ni kuka da kwalla ganin yadda aka cusawa mutane kiyayyar Shi’a da karairayi marasa tushe.
Daga baya na sake gane menene hikimar da ta sanya bayan an gama gaya maka karairayin za a ce da kai ya halatta kayi karya dan kubutar da wani afkawa aƙidar Shia, kariya ake son bawa karyar da aka jima ana yi dan kawai a cigaba da sanya gaba da rabuwar kai tsakanin musulmi.
Wannan dalilin ya sanya daga 2010 na tattara Salafanci na sanya shi a kwandon shara domin babu komai a cikinsa sai son zuciya da tsatsauran ra’ayi. Kada ka bari wanda baya son abu yayi maka bayanin abu, ba dukkan mutane ne ke yin adalci ba ga wanda basa so.
Na zaɓarwa kaina sanin kowacce akida daga ma’abotan ta, kuma Alhamdulillahi daga ɗan abinda na sani nake ƙaddara fahimtar kowa, zan karɓa abinda na gamsu gaskiya ne daga kowanne janibi, zan kuma watsar da abinda naga ya saba da hakika.
Ina shawartar ɗaliban ilimi da su karanta littafin nan da kuma wasu daga littafan Muhammad Attijaniy Assamawiy kamar: “Ask those who know” “The Shi’a are the real Ahlussunnah” “All solutions are with Prophet’s Progeny” da kuma “To be with the truthful”, hakika sai samu ƴancin tunani daga karairayin da aka kitsa a addini dan kawo rarrabuwar kan musulmi.