LABARAI/NEWS

MIJIN WATA PASTUWA YA KAI MATARSA LAHIRA

MIJIN WATA PASTUWA YA KAI MATARSA LAHIRA…

Wani labari da ke jan hankali a kafafen sada zumunta masu magana da harshen turanci shine na mutuwar wata shahararriyar mawakiyar addinin kirista mai mukamin Manzanci a rukunin Cocin zamani mai tashe da ake kira DUNAMIS.

Mawakiyar kuma manzuwar Kiristoci Osinachi Nwachukwu ‘yar shekara 42 na tsaka da tashe a bangaren wakokin Gospel inda ko a kwanakin nan an kalli wata wakarta mai taken NARA EKELE wato “Ubangiji amsa kirarina” wajen sau Milyan 72 har da yan kai a YOUTUBE kadai
Sai dai duk wannan shahara, tashe, kudi, Ilmi, daraja da matar nan ta samu bai hana ta fadawa karkashin mummunar kaddarar auren miji mai duka ba.

Wannan Miji mr Nwachukwu wanda matar tasa ke kiransa iyalinta kuma manajanta ya kasance mai matukar kishin wannan ci gaba da matarsa ke samu ta inda duk wani motsi da zata yi ya kan kulle ta a gida ya baiwa yaransu kuma yayanta bulala su taya shi dukanta, a haka suke rayuwa dukan safe daban na dare daban har zuwa ranar da tsautsayi ya gifta inda ya dake ta a kahon zuciya ta fadi magashiyyan, aka kaita asibiti ta kwana biyar bata san wa ke kanta ba har ta koma ga mahalicci…

Wani abin jan hankali shine a tsawon rayuwar auren ma’auratan matar tayi kokarin boye aibin mijinta ga duniyar kusa da ta nesanta ta inda ba a farga da lallai tana iya zama shi ya kashe ta ba har sai da labarin yadda ya dake ta a studio gaban yaranta ya fito kan cewa ya ce ta rubuta wata waka cikin harshen turanci amma ta rubuta ta da harshen Ibo. Da ga nan ne mutane suka fara tattaro abubuwanda suka shaida akan wannan auren da wannan mata bata fadi, ciki kuwa har da yawan yin waka me muryar kuka cikin hawaye da neman dauki daga Allah ta inda sau tari idan tana waka a coci kowa kan taya ta kuka ba gaira ba dalili saboda yanayinta.

Wani abin karin jan hankali shine yadda Fastoci maza da mata suka dauki hanyar sauya salon wa’azinsu na da mai kira ga ma’aurata da su rika boye matsalolin aurensu inda a yanzu suke kira da a fara fadin matsalar aure musamman idan ta zamo ta duka ce, ko don a sami ceton rai, domin Mijinda zai daki matarsa ya sa yaranta su dake ta duk da ta fi shi duk wata daukaka da karfi amma bata bari an sani ba har sai da ya kashe ta to lallai ba karamin zurfin ciki ne da matar ba…

Labarin ya ja hankalina bayan da ya tuna min yadda wani miji a gabana ya ce da matarsa “wance zo ki ji” ta tashi ta bi shi, bayan kamar minti talatin ta dawo ta zauna muka ci gaba da hira, sai washe gari da tafiya ta hada ni da shi babu ita a cikin jirgi zuwa Lagos ya ke ce min in rika yi mata fada don jiya da ya kirata a gabana din nan fa duka ya je yayi mata ya jira ta share ido sannan ta fito… A lokacin ba dukan nasa ba ne ya fi jan hankalina ba kamar dalilin kiranta a je a doketan wanda ban gani ba a iya zamana tare da su na kwana3.
Kwarai ina yabawa yan Arewa wajen rashin saurin hannu na dukan mata, amma kadan din da suke yi su yi wa Allah su Kiyayi social media wadda bata tufa asirin duk wani me aika aika…
Mu sha ruwa lafiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button